"Saboda Biredi": Budurwa Yar Najeriya Ta Bayyana Dalilin Rabuwa da Saurayin Da Ya Nuna Yan Sonta

"Saboda Biredi": Budurwa Yar Najeriya Ta Bayyana Dalilin Rabuwa da Saurayin Da Ya Nuna Yan Sonta

  • Wata budurwa ƴar Najeriya ta bayyana dalilinta mai ban mamaki na rabuwa da wanda ya nuna yana sonta
  • A cewar budurwar, ta yanke shawarar daina kula shi ne saboda kullum ba ya da wani abinci sai biredi kawai
  • Masu amfani da shafukan sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu game da abin da budurwar ta yi, inda wasu suke ganin abin dariya ne

Wata budurwa ƴar Najeriya mai amfani da sunan @kaaego a kan manhajar X (wacce a baya aka fi sani da Twitter) ta faɗi dalilin da ya sa ta daina kula wani da ya nuna yana sonta.

A cewarta, dole ce ta sanya cikin gaggawa ta yanke duk wata alaƙa da ke tsakaninta da shi.

Budurwa ta rabu da saurayinta saboda cin biredi
Budurwa ta rabu da saurayinta saboda kullum biredi ya ke ci Hoto: Kaaego/X, Miodrag Ignjatovic/ Getty Images (Hoton saurayin an yi amfani da shi ne kawai domin yin misali)
Asali: UGC

Budurwa ta kaɗu saboda yawan cin biredin mai sonta

Kaaego ta bayyana cewa ta yanke shawarar ne sakamakon binciken da ta yi game da saurayin, inda ta gano cewa kullum cikin cin biredi yake.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yan Mata Fiye Da 10 a Kan Babura Ya Girgiza Intanet, Sun Jeru Sanye Da Anko

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk lokacin da ta tambayi saurayin abin da ya yi karin safe da shi ko abincin da ya ci da rana, sai ya gaya mata cewa biredi ya ci, wanda hakan bai yi mata daɗi ba.

Kaaego ta bayar da labarin abin da ya faru ne lokacin da take mayar da martani kan wata tambaya da aka yi ta cewa:

"Yaushe ku ka gane cewa ba za ku iya rayuwa da su ba lokacin da ku ke tsaka da ƙoƙarin ƙulla alaƙa?"

Ta cigaba da cewa lokacin da ta duba ko sau nawa ya rubuta mata kalmar biredi a hirarsu ta gano cewa, ya rubuta kalmar har sau 42.

Ta wallafa a shafinta na Twitter cewa:

"Wallahi, duk lokacin da na tambayi abin da ya ci, kullum sai ya ce min biredi."

Wane irin martani ƴan soshiyal midiya suka yi?

Kara karanta wannan

"Kada Ka Bar Ta Da Yunwa": Mahaifin Amarya Ya Gargadi Ango, Ya Mayar Masa Da Kudin Sadaki a Wajen Biki

Masu amfani da yanar gizo sun bayyana ra'ayoyinsu game da halin da budurwar ta tsinci kanta a ciki da hukuncin da ta yanke na kawo ƙarshen batun soyayyarsu.

Hemiloluwa ya rubuta:

"Mutum ba zai iya cin biredi cikin kwanciyar hankali ba?"

Canny Brainny ya rubuta:

"Ina fata kin gaya masa "mutum ba zai rayu da biredi kaɗai ba" kafin ki rabu da shi."

Jet Daniel ya rubuta:

"Ina cin biredi a kowace rana lokacin da na ke saurayi ba wai domin ba ni da kuɗi ba, kawai ba ni da lokacin da zan dafa abin da na ke so ne, saboda ko da yaushe ina aiki, idan da kina da wayau a nan ne ya kamata ki shigo rayuwarsa, ki mayar da shi cikakken mutum."

Zee Lee ya rubuta:

"Wannan iri na ne, gaskiya bazan iya kwana biyu ba, ba tare da cin biredi ba."

Ta yi kuskure

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wata budurwa mai suna Rachel Halilu wacce ta bayyana cewa abin da budurwar ta yi kuskure ne.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ainihin Dalilan Da Suka Sanya Aka Dakatar Da Shirin N-Power

A ganinta cin biredi a koda yaushe bai kai dalilin da zai sanya a rabu da wanda ya nuna yana son ƙulla alaƙa ta soyayya da kai ba.

Ta bayyana cewa abin da kawai zai sanya ta rabu da wanda ya nuna sonta shi ne idan ba ya ganin mutuncinta da na iyayenta, sannan ya kasa nuna mata kulawar da ta dace.

Mahaifin Amarya Ya Ja Kunnen Ango

A wani labarin kuma, wani mahaifin wata amarya ya gargaɗi wanda ya auri ɗigarsa da ka da ya kuskura ya bar masa ita da yunwa.

Mahaifin amaryar ya dawo masa da kuɗaɗen sadakin, inda ya gaya masa cewa ya ya yi amfani da su wajen kula da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng