Matashi Ya Bude Asusun Banki Ga 'Ya'yan da Zai Haifa Su 6 Nan Gaba Don Su Zama Masu Arziki

Matashi Ya Bude Asusun Banki Ga 'Ya'yan da Zai Haifa Su 6 Nan Gaba Don Su Zama Masu Arziki

  • Attajirin matashi ya bayyana burinsa na adana makudan kudade ga yaran da zai haifa nan gaba
  • Ya ce ya na burin adana musu Naira biliyan 22 inda ya ce a yanzu ya adana musu fiye da Naira biliyan 2
  • Ya ce burinsa shi ne ko wane daga cikinsu ya mallaki Naira biliyan 122 idan ya kai shekaru 21 inda ya ce 'ya'ya shida zai haifa

Wani matashi ya nemo hanyar azurta 'ya'yansa da bai haifa ba inda ya fara adana musu kudade.

Matashin mai suna @hqgotrich ya ajiye fiye da Naira biliyan 2 inda ya ke son adana musu Naira biliyan 122 zuwa girmansu.

Attajirin matashi ya fadi adadin kudaden da zai adana wa 'ya'yansa
Matashin ya bayyana dalilinsa na yin hakan. Hoto: @hqgotrich.
Asali: TikTok

Meye matashin ke cewa kan 'ya'yan nasa?

Ya ce ya kamata mutane su gane amfani da asusun 'Trust Fund' don taimakawa yaransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Isra'ila Ta Yi Wa Tinubu Alkawarin Ba Da Kariya Kan Rikicin Kasar Da Falasdinu, Ta Fadi Dalilai

Ya ce ya na bukatar bai wa ko wane yaro fiye da Naira biliyan 120 idan ya cika shekaru 21.

Dan kasuwar ya ce ya na da burin kawo sauyi a bambancin da ke tsakanin bakaken fata da farare.

Ya ce:

"Babban buri na shi ne bai wa 'ya'yana wata dama a duniya ganin yadda su ke da kalubale a matsayinsu na bakaken fata."

Ku kalli bidiyon a kasa:

Mutane da dama sun yi martani inda su ke yabon matashin ganin yadda ya nuna kauna ga yaran tun kafin a haife su.

Legit ta tattaro muku martanin mutane kan wannan shiri na matashin:

Michaelina:

"Ina ma ace ina da mahaifi kamar kai, da na zama uwa da za ta yi haka."

LALA said:

"Kai gaskiya ba na kokari, ka fada min yadda zan tara Dala miliyan uku."

Tacha.B:

"Kai gaskiya wannan abin burgewa ne."

Kara karanta wannan

Wike Ya Kafa Doka Kan 'Yan Bola Jari Da Masu Baban Bola Shiga Yankunan Abuja, Ya Fadi Matakin Gaba

brandonswealth:

"Wannan shi ne abin da na ke son yi wa 'ya'yan da zan haifa."

Richard Mwai467:

"Ya na da kyau ka taimaki 'ya'yanka amma ka koya musu neman na kansu ya fi."

Budurwa ta haura katanga don isar da sakon gulma

A wani labarin, wata budurwa ta girgiza Intanet bayan tsallaka kofar shiga gida don kawai ta kai gulma.

Matar gidan a bangarenta ta taimaka wurin saka mata matakala don saukowa lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.