Mahaifin Amarya Mayar Da Kudin Sadakin Yarsa Ga Ango, Ya Ce Ya Kula Da Ita Sosai

Mahaifin Amarya Mayar Da Kudin Sadakin Yarsa Ga Ango, Ya Ce Ya Kula Da Ita Sosai

  • Mahaifin amarya ya sosa zukata yayin da ya mayar da kuɗin sadakin amaryar ƴarsa, ya kuma yi wa ango gargaɗi
  • Mutumin ya gargadi ango game da illar da ke tattare da barin ƴarsa da yunwa da rashin kula da ita
  • Da yawan mutanen da suka kalli faifan bidiyon sun yabawa mahaifin amaryar, yayin da wasu suka yi magana kan yadda bikin aurensu ya kasance

Yayin daurin aure mahaifin wata amarya ya ɗauki naira 1k kacal ya mayarwa ango ragowar sadakin amarya.

A cikin wani faifan bidiyo da aka gani a TikTok, mahaifin amaryar ya matso kusa da angon ya roke shi da ya kula da ƴarsa sosai.

Mahaifin amarya ya mayarwa ango kudin sadaki
Mahaifin amaryar ya bukaci ya kula masa da yarsa Hoto: @preciousbee_alaga
Asali: TikTok

Ya gargadi ango akan illar barin ƴarsa da yunwa

Mahaifin amaryar ya ce ya mayar da kuɗin ne kuma yana sa ran angon zai yi amfani da su wajen siyan duk wani abu da zai yi amfani da shi wajen kula da ƴarsa.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Farmaki a Jihar Arewa, Sun Yi Awon Gaba Da Manoma Masu Yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi barazanar ƙwace ɗiyarsa idan ango ya kasa sauke nauyin da ke kansa.

Mahaifin amaryar ya bayyana cewa:

"Tare da gargadi don Allah ka kula da ƴarmu, kada ka barta da yunwa, wannan kuɗin mun ba ka don ka ƙara duk abin da za ka yi domin tabbatar da cewa ba za ta taɓa jin yunwa ba, domin idan ka yi haka za mu zo mu karɓe ta. Saboda muna sonta sosai."

Jama'a sunyi tsokaci akan abin mahaifin ya yi

Dubem ya rubuta:

"Kada wani suriki ya zo ya yi min irin wannan maganar, saboda ni da zan yi aure na san yadda zan tsarawa kai na. Menene kuma na yin gargaɗi."

user2610750564128 ya rubuta:

"Haka ma ake yi a ƙasar Yarbawa, mukan mayar masa da sadaki mu gaya masa cewa ba siyar da ita muka yi ba, amma ya kamata ya kula da ita."

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kwararawa Malalacin Mijinta Ruwa Yana Cikin Bacci, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Bitrus Bulus ya rubuta:

"Kwatsam yanzu haka kowa mahaifi yake yi, su wanene wadanda suka karbi manyan miliyoyin?"

Canadian_emmanuel ya rubuta:

"Wannan ai surutu ne kawai. Sun tattara kayayyaki miliyoyin kuɗi. Kuna wasa ko?"

Greg Jessica ta rubuta:

"Wannan hakika al'ada ce a tsakanin mutanen ƙabilar Bendel (Edo da Delta). Ba wai kawai game da mutumin da ke cikin bidiyon ba."

Merry py ta rubuta:

"Wannan ba zai taba zama bikin auren Igbo ba, har ma da koɗar ka sai sun karɓa."

Matashi Ya Koka Kan Cin Amanar Budurwarsa Ta Yi Masa

A wani labarin kuma, wani matashi ya nuna takaicinsa kan yadda budurwar da zai aura ta ci amanarsa da maza biyar.

Matashin ya bayyana cewa ya rasa matakin ɗauka kan budurwar tasa bayan wannan cin amanar da ta yi masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng