Abdulrahman Sani Yakubu: Malamin Najeriya Da Yake Aiki a Ka’aba a Saudiyya

Abdulrahman Sani Yakubu: Malamin Najeriya Da Yake Aiki a Ka’aba a Saudiyya

  • Abdulrahman Sani Yakubu ya yi bayanin yadda ya tsinci kan shi ya na aiki a masallacin Ka’aba
  • Malamin musuluncin ya yi digiri har uku a masallacin jami’ar musulunci da ke kasa mai tsarki
  • Bayan fara aiki a Abuja sai aka yi masa tayin ya yi aiki a Saudi Arabiya, bai yi wasa da damar ba

Jihar Kaduna - Abdulrahman Sani Yakubu ya yi hira da BBC Hausa a shirin ‘ku san malamanku’, a nan ya yi bayanin takaitaccen tarihin rayuwarsa.

An haifi Dakta Abdulrahman Sani Yakubu ne a garin Zariya, inda ya halarci makarantar firamare kuma ya fara sakandare a makarantar nan ta Barewa.

Daga baya ne ya ce iyayensa su ka karkata akalar karatunsa zuwa ga addini, saboda haka ya koma makarantar sakandare ta Sheikh Abubakar Gumi.

Kara karanta wannan

Yadda Binciken Da Tinubu Yake Yi Zai Tona Barnar da Buhari Ya Yi – Kanal Dangiwa

Abdurrahman M. Sani Yakubu
Babban Malami, Dr. Abdurrahman Sani Yakubu Hoto: Abdurrahman M. Sani Yakubu
Asali: Facebook

Tafiya Saudiyya a ajin karshe

Bayan ya karasa sakandare, Abdulrahman Yakubu ya tafi jami’ar musulunci ta Nijar domin karanta Ilmin Shari’a, har ya kai ajin karshe watau hudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A shekarar da ya kamata ya gama ne sai malamin ya samu gurbin karatu a jami’ar musulunci da ke birnin Madina, sai ya hakura da karatun shari’a.

Samun aiki a Masallacin Ka'aba

Da malamin ya samu kan shi a Saudiyya, ya yi digiri uku tun daga na farko zuwa PhD a fannin akida, da ya gama karatu sai ya dawo kasarsa.

A tattaunawar da aka yi da shi, shehin malamin ya bada labarin yadda ya samu kan shi ya na aiki a masallacin Ka’aba da ke Makkah a Saudiyya.

Abdulrahman Sani Yakubu ya na zaune, aka zo aka same shi takanas da tayin aiki a masallaci mai tsarki, tuni malamin akidan ya yi na’am da hakan.

Kara karanta wannan

Rayuwa Juyi-Juyi: Na Taba Yin Gadi, Ilmi Ya Jawo Na Zama Shugaban Kasa - Tinubu

"Ina aiki a ka’aba a masallacin Allah (SWT) mai girma, musamman ina zaune, aka zo aka tambaye ni ko zan yi, na ce zan yi.
Ni ne shugaban sashen Hausa na masallacin harami – dakin Allah (SWT) mai alfarma."

- Abdulrahman Sani Yakubu

Malaman Abdulrahman Sani Yakubu

Da aka yi masa tambaya game da malamansa a rayuwa, sai ya ce wanda ya fara karantar da shi a duniya shi ne mahaifinsa, Sheikh Sani Yakubu.

Babban malamin ya yi karatu a hannun baffansa, Malam Abdulkadir Yakubu, baya ga haka ya yi ilmi a zaurori da islamiyyu da sauran makarantu.

A taimakawa talakawa - Sarkin Kano

An rahoto Aminu Ado Bayero ya na cewa ba za su gaza wajen kira ga gwamnati ba, ana sanar da ita wahalar da mutane ke sha saboda tsadar rayuwa.

Sarkin Kano ya yi kira ga attajirai a al’umma su taimakawa masu bukata saboda yunwa da halin tattalin arzikin kasar ya jawo ana cikin kangi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng