Fasto Ya Shawarci Maza Su Auri Mata Fiye Da Daya Don Tsawon Rai, Bidiyon Ya Yadu
- Wani Fasto ya girgiza jama'a inda ya ke bai wa Kiristoci shawara su auri mata fiye da daya ba matsala ba ne
- Faston mai suna Meshack Aboh ya ce idan mutum ya na son ya yi tsawon rai a duniya to ya kamata ya auri mata fiye da daya
- Ya ce shi yanzu haka ya na da mata biyu kuma zai ci gaba da wayar da kan 'yan uwa a kan muhimmancin hakan
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Accra, Ghana – Wani Fasto mai suna Meshack Aboh ya bukaci mazaje da su auri mata hudu idan suna so su dade a duniya.
Aboh ya yi wannan kira ne kan auren mata hudu a wani shiri na UTV a ranar Asabar 19 ga watan Agusta, Legit.ng ta tattaro.
Meye Faston ya ce?
Faston ya kasance mai mata ne fiye da daya sabanin sauran Kiristoci da addininsu ya haramta hakan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Faston ya yi kira musamman ga Kiristoci da cewa kada su ji komai idan su na sha’awar auren mata fiye da daya.
Ya bayyana cewa auren mata fiye da daya al’adar Turawa ce da kuma kasar Ghana, inda ya ce yanzu haka ya na da mata biyu.
Ku kalli bidiyon Faston a kasa:
Mutane da dama sun mai da martani kan maganar Faston
Accomplish Man:
"Ba laifi ba ne, ubangiji ya maka albarka."
Sturdd Ibrakadabra Munffins:
"Wannan shi ne gaskiya."
Mickey Ashanti:
"Ubangiji ya albarkaci wannan Fasto."
Priscilla Annang:
"Ubangiji ka kawo mana sauki."
Adwoa Xendigiri:
"Auren mata da yawa ba wasa ba ne, idan za ka dauki nauyinsu da 'ya'yansu da samar da zaman lafiya ba komai."
John Ofori:
"Ubangiji ya maka albarka Fasto."
Bidiyon Santala-Santalan 'Yan Mata Na Leburanci Ya Yadu
A wani labarin, mutane sun girgiza yayin su ka gano faifan bidiyon kyawawan 'yan mata na leburanci wanda ba a saba ganin hakan ba.
'Yan matan guda biyu na kwaba siminti tare da dibar bulok don kai wa wata budurwa da ke yabe a jikin gini.
Mutane da dama sun yabi kwazon 'yan matan yayin da wasu ke musu gargadi kan kare lafiyarsu na saka kariyar hannu da kafa.
Asali: Legit.ng