Matashi Ya Soke Aurensa Da Budurwarsa Saboda Ta Bukaci Sai An Yi Biki Na Kece Raini
- Wani matashi ya fasa auren budurwarsa wacce ta haƙiƙance sai sun yi biki na gani na faɗa domin a kece raini
- Budurwar wacce zai aura ta gaya masa cewa tana son su yi bikin kece raini wanda zai laƙume aƙalla N17m
- Nan da nan matashin ya rabu da budurwar sannan ya koma ƙasar Singapore, inda ya ce akwai hanyoyin da suka dace kan yadda zai kashe N17m
Wani matashi ya soke auren da yake shirin yi tare da rabuwa da wacce zai aura ana sauran kwanaki kaɗan a gudanar da bikinsu.
Matashin dai ya bayar da labarin na sa ne a wani ɓoyayyen saƙo da ya tura wa wani mai faɗa a ji a Twitter, mai suna Wizarab.
Matashin ya yi bayanin cewa budurwar ta buƙaci a gudanar da biki na kece raini, wanda zai sanya ya kashe maƙudan kuɗi har N17m.
Ya bayyana cewa bai shirya kashe waɗannan maƙudan kuɗaɗen ba a wajen biki, saboda hakan asara ce.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Matashin ya shilla Singapore bayan ya rabu da budurwar
Daga nan kawai, sai ya rabu da wacce zai aura ɗin sannan ya koma ƙasar Singapore ba tare da ita ba.
Matashin ya bayyana cewa iyayenta sun yi ta kiransa a waya domin neman hanyar da za a sasanta tsakaninsu, amma ya yi biris da kiraye-kirayen da su ke masa.
Matashin ya bayyana cewa:
"Na fasa auren, kuma mahaifina ya goya min baya, inda ya ce ya yarda da duk matakin da na ɗauka. Iyayenta suna ta kirana domin a sasanta amma na ƙi ɗaukar wayar su."
Martanin masu amfani da Twitter
@Wizarab10 ya rubuta:
"Ta ce ba za ta aure shi ba idan bai kashe N17m ba akan bikin da take mafarkin samu. Ko sisi ba za ta bayar ba wato saboda namiji ne ke da alhakin ba mace irin bikin da take mafarkin samu."
Auntyadaa ta rubuta:
"N17m kawai saboda biki? Ko wani abu? Ban gane ba."
@EgwuSamuel49 ya rubuta:
"Na san za ka buƙaci wani iri na ya biyo ka zuwa Singapore domin riƙa zuba maka ruwa a kanka har sai ka huce."
Budurwa Ta Kai Karar Saurayinta Kotu
A wani labarin kuma, wata budurwa ta kai ƙarar saurayinta gaban hukuma bisa zarginsa da cinye mata kuɗaɗe.
Budurwar ƴar jihar Kano ta maka saurayin na ta ƙara ne a gaban kotu saboda yaudarar ta da ya yi, inda ya sanya ta yi ta kashe masa kuɗaɗe.
Asali: Legit.ng