Ya Yaudare ta Bayan ta Kashe Masa N0.9m, Mace ta Shigar da Karar Saurayi a Kotu

Ya Yaudare ta Bayan ta Kashe Masa N0.9m, Mace ta Shigar da Karar Saurayi a Kotu

  • Ana shari’a da wani Hassan Umar a karamin kotu na majistare da ke Kano a kan rikicin soyayya
  • Tsohuwar masoyiyar wannan mutumi ta shigar da kara a kotu, ta na mai zarginsa da yaudararta
  • Da ya cinye mata dukiya a soyayya, matar ta ce wanda ya yi niyyar aurenta ya daina zuwa wurinta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Wani bawan Allah mai suna Hassan Umar ya na gaban kotun majistare a jihar Kano, a sakamakon kara da aka maka shi.

A wani labari da ya fito a Daily Trust, an ji cewa Hassan Umar zai amsa laifin yaudarar budurwarsa bayan ta kashe masa kudi.

Matar da ta shigar da kara ta fadawa Alkali yadda ta batar da N900, 000 a kan Umar a lokacin da su ke soyayya, da shirin zai aure ta.

Kara karanta wannan

Saurayi Ya Hana Budurwa Shiga Gidansa Bayan Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Ya Mata Bidiyo

Masoya
Hoton wasu masoya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An saba alkawarin yin aure

Lauyan mai kara ya yi ikirarin bayan an cinye mata kudi, mutumin ya yaudare ta, ya ki yarda ya aure ta kamar yadda aka yi alkawari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar mai shigar da kara, Umar ya dauke kafa daga zuwa hira a wajenta kamar yadda ya saba, duk da ya mori abinci da kayan dadi.

Wanda ake tuhuma bai amsa laifi ba

Kamar yadda rahoton ya tabbatar, da aka karantowa wannan mutumi laifin da yake wuyansa, sai ya fadawa Mai shari’a sam bai da laifi.

Salisu Hussaini wanda shi ne Alkali da ke sauraron karar a kotun na majistare ya bukaci kowane bangare ya gabatar da shaidu a kotu.

Za a saurari shaidun da aka gabatar a zama na gaba da kotun za ta yi domin cigaba da shari’ar.

Kara karanta wannan

Mata Ta Shiga Rudani Bayan Kotu Ta Yi Hukunci Kan Zargin Cizon Mai Musu Sulhu, Alkali Ya Yi Bayani

Da ta ke magana bayan zaman da aka yi, wannan mata dai ta zargi tsohon masoyinta da yi mata asiri

"Ba na tunanin ba asiri ya yi mani ba. Duka abin da ya tambaye ni sai in yi masa nan-take.
Na dafa masa abinci iri-iri, har da kaji, nama har da raguna biyu. Na kashe fiye da N900, 000 a kan shi.
Daga nan kuma sai ya fara nuna mani kamar bai damu ba. Daga baya kuma ya daina zuwa wuri na."

- Inji mai kara

Man fetur zai tashi

Ku na da labari shugaban IPMAN ya ce matuƙar dalar Amurka za ta tashi, dole ne farashin man fetur zai tashi sama a gidajen mai.

Shugaban ƙungiyar IPMAN ya ce dillalan mai ba su iya samun dala a bankunan, idan aka je hannun ‘yan canji kuwa $1 ta haura N920.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng