“Ku Koma Najeriya”: An Kori Dalibai 3 Daga Jami’ar Burtaniya Kan Biyan Kudi Makaranta A Latti

“Ku Koma Najeriya”: An Kori Dalibai 3 Daga Jami’ar Burtaniya Kan Biyan Kudi Makaranta A Latti

  • Wasu 'yan Najeriya dalibai su uku sun gamu da matsala bayan jami'ar Swansea da ke Burtaniya ta koro su gida
  • Daliban sun bayyana dalilin korar ta su da cewa sun biya kudin makaranta ne sa'o'i kadan bayan an kulle biya
  • Wani a cikinsu ya ce filayen mahaifinsa ya siyar don biyan kudin amma sun rike kudin kuma suka ce su dauki jakansu su dawo Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

An cire wasu 'yan Najeriya su uku daga jerin daliban jami'ar Swansea da ke Burtaniya bayan biyan kudin makaranta ba a kan lokaci ba.

Daliban sun hada Omolade Olaitan da Emmanuel Okohoboh da kuma Paulette Ojogun wadanda suka biya kudin sa'o'i kadan bayan an rufe biyan kudin, Legit.ng ta tattaro.

Daliban Najeriya 3 da aka koro gida saboda biyan kudin makaranta latti
An Cire Sunayen Daliban A Jami'ar Swansea Kan Biyan Kudi Makaranta A Latti. Hoto: ITV.
Asali: UGC

Daliban sun bayyanawa makarantar cewa suka samu matsalar kudin ne saboda sauya fasalin Naira da aka samu a farkon shekarar nan.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar

Me jami'ar ta ce kan daliban?

Amma jami'ar ta yi kunnen uwar shegu tare da rike kudin har Naira miliyan 3 da dubu 800 tare da umartansu da su tattara kayansu su koma Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daya daga cikin daliban Omolade Olaitan ta ce:

"A ranar 29 ga watan Maris na samu sakon cewa tun da ban biya kudin makarantar a kan lokaci ba, ba za su iya bari na a jami'ar ba don haka na tattara kaya na, na koma kasa ta."

Daya dalibin mai suna Emmanuel Okohoboh ya ce sai da ya siyar da filaye guda biyu kafin ya samu kudin yin digiri na biyu.

Ya ce:

"Babu adalci kuma ba su da tausayi, sai da na siyar da filayen mahaifi na biyu kafin samun wannan kudade."

Meye daya daga cikin daliban ke cewa?

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Jawowa El-Rufai, Danladi Da Okotete Samun Tasgaro a Zama Ministoci

Yayin da daliba Paulette Ojogun ta barke da kuka a faifan bidiyo da ITV ta wallafa.

Ta ce:

"Ina murna da jin dadi na zo nan, me yasa za ku kwace wannan farin ciki daga gare ni, saboda na biya kudi latti? Na tura sakon e-mail amma shiru har yanzu."

Legit.ng ta tura sakon e-mail a kokarin jin ta bakin jami'ar amma har yanzu babu martani.

Daliban Najeriya Daga Sudan Sun Makale A Hanya

A wani labarin, wasu daga cikin daliban Najeriya sun makale a tsakiyar Hamada yayin kokarin dawowa gida.

Bayan an samu tsagaita wuta na 'yan kwanak a kasar Sudan, kasashe da dama sun bazama kwaso 'yan kasarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.