Sana’a Sa’a: Farfesa A Najeriya Ya Raba Kafa, Ya Rungumi Wanzanci Da Koyarwa A Jami’a

Sana’a Sa’a: Farfesa A Najeriya Ya Raba Kafa, Ya Rungumi Wanzanci Da Koyarwa A Jami’a

  • Farfesa Bashir Aliyu Sallau ya dade da sana’ar wanzanci inda ya ce ya cire girman kai ne don rufawa kansa asiri
  • Farfesan na koyarwa ne a tsangayar Hausa a jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsin-Ma a jihar Katsina
  • Ya bayyana yadda sana’ar ta rufa masa asiri musamman a lokacin da malaman jami’o’i su ka tafi yajin aiki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Katsina – Wani Farfesa a jihar Katsina mai suna Bashir Aliyu Sallau ya ba wa mutane mamaki inda ya rike sana’ar wanzanci bayan kasancewar shi malamin jami’a.

Farfesan na koyarwa ne a sashen Hausa na jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsin-Ma a jihar Katsina.

Farfesan da ya rike sana'ar wanzanci don rufawa kansa asiri
Farfesa Bashir Sallau Kenan Mai Sana'ar Wanzanci A Najeriya. Hoto: DW.
Asali: UGC

Malamin ya bayyana yadda ya rike sana’ar wanzanci da kuma ba da magani inda ya ce ya fahimci akwai arziki a sana’ar wanzanci.

Ya bayyana yadda sana'ar wanzanci ta rufa masa asiri

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Shugaba a APC Ya Yi Murabus Yayin da Ganduje Ya Karbi Jam’iyya

Farfesan ya bayyana haka ne yayin hira da DW Hausa a jiya Alhamis 3 ga watan Agusta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce sana’ar wanzanci ce ta rike shi lokacin da aka tafi yajin aiki na malaman jami’o’i na tsawon lokaci tare da kin biyansu albashi.

Ya ce da ace bai iya sana’ar wanzanci ba a wancan lokaci bai san ya zai yi ba, ya ce hakan ne ya kara masa karfin gwiwar rike sana’ar ba tare da girman kai ba.

Ya ce:

“Kowa yasan koyarwa a jami’a da lokacin da ake ba wa kowa ya je ya koyar, ba kaman sauran aikin gwamnati ba ne da za a ce ka je karfe 8:00 zuwa karfe 3:00 ko 4:00 ka taso.
Idan na gama lakca ina wuce wa wanzanci ko kuma kafin na tafi karfe 7:00 na je wanzanci zuwa 10:00 sai na wuce jami’a.”

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Abba, Abokan Arziki Sun Tuna da Dadiyata Bayan Shekaru 4 da Bacewa

Ya ce akwai arziki sosai a sana'ar wanzanci

Farfesan ya ce zai ci gaba da sana’arsa saboda muhimmancinta:

“Tun kafin bature ya zo kasar Hausa, mu na da sana’oi daban-daban a kasar Hausa da suke taimaka mana bunkasar tattalin arziki.
“Na fahimci a cikin wanzanci akwai arziki, saboda malaman jami’a sun tafi yajin aiki, gwamnati ta tsayar da albashi amma da ban daurawa kai na girman kai bai, na ci gaba da yi.
“Idan na fito da zabira ta wuraren da aka haihu, ina samun abinda zan biyawa kai na da iyali na bukatu, hakan shi ya karamin karfin gwiwar riko da sana’ar.”

Farfesa Ya Bukaci FG Ta Gudanar Da Kidayar Dabbobi Don Sanin Adadinsu

A wani labarin, wani Farfesa a Najeriya ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da kidayar dabbobi don samun ci gaba.

Farfesa Olajide Babayemi na jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo shi ya bayyana haka a Lagos yayin ganawa da 'yan jaridu a ranar 21 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Kuncin Rayuwa: Jama'a Sun Fasa Rumbun Abincin Nema a Adamawa, Za a Tsaurara Tsaro a Kaduna

Ya ce kamar yadda ake na mutane kidayar dabbobin zai taimaka wurin tsare-tsare na gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.