Kwankwaso, Abba, Abokan Arziki Sun Tuna da Dadiyata Bayan Shekaru 4 da Bacewa

Kwankwaso, Abba, Abokan Arziki Sun Tuna da Dadiyata Bayan Shekaru 4 da Bacewa

  • Abubakar Idris ‘Abu Hanifa’ ya bace tun farkon Agustan 2019, har yau babu wanda ya ji duriyarsa
  • Masoya da ‘Yanuwa sun shirya zaman addu’a a masallaci domin Allah (SWT) ya kubutar da shi
  • Gwamnan Jihar Kano ya dauki alkawari za su yi bakin kokari wajen gano inda Dadiyata ya shige

Abuja - Shekaru hudu kenan da bacewar Abubakar Idris Abu Hanifa wanda mutane su ka fi sani a shafukan sada zumunta da Dadiyata.

Legit.ng Hausa ta na cikin wadanda su ka fara kawo labari a lokacin da wasu su ka yi gaba da wannan Bawan Allah a Agustan 2019.

Har zuwa yanzu babu wani wanda ya ji labarin duriyarsa, ko ya ji inda halin da Dadiyata yake ciki, iyalinsa su na cikin wani hali.

Dadiyata
Abubakar Dadiyata a lokacin ya na kasar waje Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

An yi addu'o'i a garin Kano

Kara karanta wannan

Binani, Keyamo, Fashola Da 'Yan Siyasa 10 Da Ba Su Da Rabon Zama Ministoci

Ganin an cika shekaru hudu da dauke matashin mai ‘ya ‘ya biyu, abokan arziki da na kusa da Malam Abubakar Dadiyata sun shirya addu’o’i.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda wani amininsa mai suna Hassan Sani Tukur ya shaida, masoyan wannan Bawan Allah da ake nema sun shirya taron addu’o’i.

A wajen taron, an sauke Al-Kur’ani mai girma tare da rokon Allah (SWT) ya fito da Abubakar Dadiyata, ya sada shi da iyalinsa da danginsa.

Daily Trust ta ce an yi ibadan ne a masallacin gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ke kan titin Millar a Unguwar Bompai a garin Kano.

Tsohuwar Dadiyata ta rasu

Har zuwa lokacin da aka yi awon-gaba da shi, ya na cikin manyan magoya bayan Rabiu Kwankwaso a shafukan sada zumunta na zamani.

Ana zargin a dalilin sace Dadiyata mahafiyarsa ta rasu a Agustan shekarar bara bayan zaman takaicin shekaru uku da 'yan makonni.

Kara karanta wannan

Maryam Shetty: Nadin Jikar Sarkin Kano a Cikin Ministoci Ya Jawowa Tinubu Surutu

Mu na fatan Allah (SWT) bayyana shi

Mun zanta da Malam Hassan Sani Tukur a ranar Alhamis, ya kuma shaida mana cewa su na fatan abokinsu ya bayyana, kuma ya dawo gida.

"Kamar yadda Gwamna (Abba Kabir Yusuf) ya yi albishir, ana binciken Dadiyata. Tun rantsar da shi ya yi alkawarin za su yi wannan.
Mu na fatan za a samu mafita kan halin da yake ciki. Saboda yanayin yadda aka yi gaba da shi, binciken da ake yi ya na bukatar sirri."

- Hassan Sani Tukur

A jiya an ji Gwamnan Kano, Mai girma Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso duk sun yi magana game da halin babban masoyin na su.

"Ya kamata 'Yan majalisa su yi magana"

Kwanakin baya aka ji labari, Kwamred Shehu Sani ya tofa albarkacin bakinsa kan mutuwar mahaifiyar Abubakar Dadiyata a garin Kaduna.

Tsohon Sanatan ya yi addu’a ga Ubangiji ya jikan wannan mata, ya bukaci ‘Yan majalisar tarayya su kawo maganar matashin wajen aikinsu.

Kara karanta wannan

PDP da daukar aiki? Jama'a sun yi mamaki yayin da PDP ta ce za ta dauki aiki mai girma

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng