Matashin Da Ya Fadawa Fasto Laifin Da Ya Aikata A Baya Ya Sha Dauri, Mutane Sun Yi Martani
- Fasto ya kama wani matashi tsohon mamban majami’arsa bayan mamban ya fada masa laifin da ya taba aikatawa
- Matashin ya fadawa Faston cewa lokacin da ya ke zuwa majami’ar ya taba satar kudi har N450,000 na kudin baiko
- Da jin wannan magana sai Faston ya harzuka tare da kiran ‘yan sanda suka kama matashin da cewa sai ‘yan uwansa sun biya
Wani matashi a Najeria ya yi dana sanin aikata laifi bayan ya yi ta maza wurin bayyanawa Fasto abin da ya yi.
Matashin ya fadawa Faston cewa ya taba satar N450,000 daga kudaden baiko lokacin da yake zuwa majami’ar a matsayin mamba, Legit ta tattaro.
Ya ce ya yi tunanin fadan abin da ya aikata a baya zai sa Faston ya yafe masa amma sai Faston ya sa ‘yan sanda suka kama shi.
Wole Soyinka Ya Goyi Bayan Davido Kan Bidiyon 'Jaye Lo': "Rawa a Gaban Masallaci Ba Tsokana Bane, Kada Ka Bada Hakuri"
Yadda Faston ya kama mamban majami'arsa
Wani mai suna Dexterouz11 shi ya yada labarin a shafinsa na Twitter da cewa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Wani makoci na ya je wurin Faston shi ya fada masa cewa ya taba satar kudi N450,000 watanni uku da suka wuce.
“Faston ya sa an kama shi kuma ya ce ba zai sake shi ba har sai ‘yan uwansa sun nemo kudin sun biya.”
Mutane da dama sun yi martini akan labarin Fasto da mambansa
@abgacollins:
“Wannan Faston ba shi da tausayi. hakan zai hana mutane fadar zunubansu a nan gaba, da ya samu wata hanya.”
@destinypaul6:
“N450,000 a wannan yanayi? ya kamata a kama dukkan ‘yan uwanka tare.”
@jujju666:
“Majami’a wuri ne da ya kamata ya zama na tsira, Faton ba shi da ikon kiran ‘yan sanda.”
@sarahhh:
“Hmm wannan ya wuce hankali na.”
Fasto Ya Yada Labarin Karya Cewa Ya Mutu Don Kada Ya Biya Bashin N3m
A wani labarin, wani Fasto mai suna, Paul Oyewole ya yi karyar ya mutu a manhajar WhatsApp saboda bashin da ake binshi.
Faston ya karbi bashin wani mutum har Naira miliyan uku saboda ya gagara biya sai ya yi karyar mutuwa.
An gurfanar da Faston a gaban kotun majistare kan zargin karbar N3m a wurin mamban majami'arsa.
Asali: Legit.ng