Ma’aikaciyar Otel Ta Tsinci Dalolin da Sun Haura N55m Amma Ta Yi Cigiya a Legas

Ma’aikaciyar Otel Ta Tsinci Dalolin da Sun Haura N55m Amma Ta Yi Cigiya a Legas

  • A sakamakon abin da ya faru, duniya ta samu labarin gaskiya da rikon amanar Kekwaaru Ngozi Mary
  • Wannan Baiwar Allah ma’aciyar otel ce a Legas da tayi tsintuwar $70, 000, amma ba ta sulale da su ba
  • A yayin da ta ke aiki a Eko Hotel & Suites, Mary ta ci karo da wannan kudi, sai ta sanar da manyanta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos - Kekwaaru Ngozi Mary ta na aiki ne a otel dinnan da yake garin Legas, Eko Hotel & Suites, a makon nan ta nuna tsantsar gaskiyarta.

Vanguard ta ce Miss Kekwaaru Ngozi Mary ta tsinci $70,000 da wani Bawan Allah ya jefar da su a otel, ita kuwa ta sa aka shiga cigiyar nemansa.

A maimakon tayi halin bera, wannan ma’aikaciya ta nuna gaskiya da amanarta, aka gano bakon nan da aka yi a otel din, aka kai masa kudinsa.

Kara karanta wannan

Yanzu: COEASU Ta Umarci Mambobinta Su Na Zuwa Aiki Na Kwanaki 2 Kadai A Sati Bayan Cire Tallafi

Jakar kudi a otel
Ma’aikaciya ta tsinc jakar kudi a otel Hoto: vanguardngr.com, shutterstock.com, tripadvisor.com
Asali: UGC

Jaka dauke da $70000

Wannan mutumi da bai bayyana sunansa ba, ya bar jaka dauke da makudan kudi a daya daga cikin dakunan wannan katafaren otel a Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin da ta ke aiki, Kekwaaru Ngozi Mary ta ci karo da jakar kudin, nan take kuwa sai ta sanar da shugabannin da ke kula da wannan otel.

Babban manajan otel din ne ya yi kokarin tuntubar wannan mutumi, da aka yi nasarar gano shi, an maida masa kudinsa da ya manta da su.

Rahoton ya ce wannan gaskiya da rikon amana su na cikin abin da ya jawo otel din ya yi fice

Manajan mai suna Danny Kioupouroglou ya ce abin da ya faru ya nuna tsantsagwaron gaskiyar wannan ma’aikaciyar ta su watau Kekwaaru.

A Eko Hotel and Suites, mu na alfahari da tsayawarmu tsayin daka a kan yin abin da yake daidai da kuma jin dadin abokin hulda.

Kara karanta wannan

An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

Mun yi imani cewa ma’aikatanmu su ne mafi girman jarinmu, kuma wannan lamari da ya da auku ya sake jaddada mana ra’ayin nan.

Shi kuwa wanda ya jefar da dukiyar nan, ya ji dadin yadda aka yi gaggawar dawo masa da kudinsa.

'Yan Najeriya na cikin wahala

Kun karanta rahotonmu cewa tsare-tsaren tattalin arziki da aka kawo sun jawo ana kokawa, amma gwamnati ta ce za a yaba nan gaba.

An fara tsoron lokacin nada Ministoci zai wuce ba tare da Bola Tinubu ya aikawa Majalisa sunayen wadanda za su shiga FEC ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel