Saniyar Ware: Yadda Musulman Inyamurai Su ke Kukan Wahala kan Addininsu a Kudu

Saniyar Ware: Yadda Musulman Inyamurai Su ke Kukan Wahala kan Addininsu a Kudu

  • Usman Isa Tochukwu yana cikin Musulman Ibo da ke ganin ana masu lamba saboda sabanin addini
  • Lauyan ya ce a dalilin addininsa ne Sanatan da yake wakiltar mazabarsa ya wulakanta shi a Majalisa
  • Amma akwai wadanda su ka yaba da irin mu’amalar da ake samu tsakanin mabiya addinai dabam

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Usman Isa Tochukwu musulmi ne da yake rayuwa a Kudu maso gabashin Najeriya, ya na cikin mutanen da ke kokawa da halin rayuwa.

Usman Isa Tochukwu wanda Lauya ne, ya yi amfani da shafinsa na Twitter, ya bada labarin muzgunwa da wahalar da ya sha saboda addininsa.

A cewar matashin, zamansa Musulmin Ibo daga Kudu maso gabas bai tsinana masa komai ba, ya kawo labarin haduwarsa da Sanatan yankinsa.

Musulmai
Wani masallacin Musulmai a Aiyepe Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

Haduwar Tochukwu da Sanatan Enugu ta Arewa

Kara karanta wannan

Jerin Fitattun Yan Najeriya 4 Da Suka Yi Aiki Da Buhari Kuma Suka Samu Sabbin Mukamai

"A lokacin ina aji uku a jami’ar Ahmadu Bello a Zariya, na rubutawa Sanata mai wakiltar mazabata, Chukwuka Utazi sa'ilin yana shugaban kwamtin yaki da rashin gaskiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Na nemi ya taimaka mani wajen sayen komfuta domin digirina, yayin da na isa Majalisa, ya jawo na yi zaman jiransa na tsawon awanni biya
Ko da ya zo zai saurare ni, sai ya bude takarda ta, abin da ya iya fada mani kawai shi ne “Kai ne UTHMAN ISA”, kuma ka ce daga “Nsukka” ka ke.
Ba mutanen Arewa na ke wakilta ba, je ka hadu da Sanatocinku na Arewa, da jin wannan sai na fusata, na fara yi masa yarenmu na “Nsukka”
Na tuna masa yadda ya zo garinmu, Alor-Agu yana yawo kamfe, musamman ya zo wajen Musulmai, amma mutumin nan ya bar ni a ofishinsa."

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fara da Kyau Amma Tun Farko na San Babu Inda Buhari Zai Je - Dattijon Arewa

- Uthman Isa Tochukwu

Idan Biyafara ta zama kasa mai cin gashin kan ta, ta balle daga Najeriya Tochukwu ya ce zai bar kasar Ibo, ya tare a Kano domin ya fi masa alheri.

Mu na zaune lafiya - Matasan Enugu

Aliyu Adamu shi ne shugaban matasan Hausawa na Enugu, ya shaida mana cewa rayuwa a Kudu akwai kalubale saboda bambancin addini da kabila.

A cewar wasu za sui ya jurewa abin da ake ganin muzgunuwa ne, amma ya tabbatar mana cewa su na zaman lafiya da asalin mazauna wannan yanki.

A duk lokacin da aka samu wani rikici, za a ga bata-gari ne daga waje, amma mafi rinjayen lokuta ya nuna ana zaune cikin lumuna a garuruwan Enugu.

"Irin wannan zaman lafiya ne ya jawo Gwamna ya kawowa Musulmai ziyara har masallaci a lokacin idi, ka ga kuwa ai mu na zaune lafiya."

- Aliyu Adamu

Kara karanta wannan

Yadda APC Ta Hana Tinubu Kudi a Lokacin Kamfe In Ji Mataimakin Shugaban Jam’iyya

Wani Muhseen Onyedịkachukwuya ce shi kuwa an hana shi takardar zama ‘dan asalin Enugu Ezike saboda shi Musulmi, har ana masu barazanar kisa.

Majalisa za ta saye motocin N40bn

Sanatocin da ke majalisa ta goma za su Toyota Landcruiser, sannan rahoto ya zo cewa za a rabawa ‘Yan majalisar wakilan tarayya motar Prado 2023.

Ana saida Landcruiser 2023 a kan N125m, Prado 2023 ta haura Naira miliyan 75. Kwamitin da ke kula da harkokin majalisar dattawa za a ba kwangilar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng