Wani Matashi Ya Kwace Dukkan Kayayyakin Da Ya Saya Wa Budurwa Bayan Sun Rabu

Wani Matashi Ya Kwace Dukkan Kayayyakin Da Ya Saya Wa Budurwa Bayan Sun Rabu

  • Wani matashi ya yi ta maza inda ya je gidansu tsohuwar budurwarsa ya kwato dukkan kayansa a gidan
  • Matashin ya je gidan ne da abokansa inda suka kwashe dukkan jakukkuna da wayar salular da ya siya mata
  • Mutane sun mai da martani inda da yawa suka yabi tunanin wannan matashi tare da ba wa mata shawara

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani matashi ya yi ta maza inda ya kwato dukkan kyaututtukan da ya yi wa budurwarsa bayan sun rabu.

A faifan bidiyon an gano saurayin dauke da jakukkuna da wayar salula tare da abokansa suna barin gidan, Legit.ng tattaro.

Matashi Ya Kwace Dukkan Kyaututtukan Da Ya Yi Wa Budurwa Bayan Sun Rabu
Matashin Yayin kwato Kayan Tare Da Abokansa. Hoto: @pulsenigeria247.
Asali: TikTok

Abokan suka ce sun raka matashin ne don kwato kayan da ya ba wa budurwar

An jiyo daya daga cikin abokansa a cikin faifan bidiyon na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

'Buroshi Da Safa Kawai': Budurwa Ta Fusata, Ta Mayar Da Kyautar Da Saurayinta Ya Mata Tsawon Shekaru 11

"Munje mun kwato dukkan kayan daga gidansu tsohuwar budurwarsa".

Ya kara da cewa abokin nasu ya bukaci ta ba shi dukkan kayan da ya siya mata bayan sun rabu.

Ya ce suna neman mai siyan dukkan kayan da suka kwato.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu akan faifan bidiyon.

user8411585619556:

"Kenan jakukkuna da wayar salula kawai ya siya mata? Dalilin rabuwar kenan, yara a soyayya."

yellownahcolor:

"Idan ta nemi rabuwa kawai ka kwashe kayanka ba komai."

Larry:

"Wasu ba soyayya suke ba, kawai neman kaya ne...da zafi amma hakan ya yi."

user18214129853981:

"Eiiiii hmmm na tuna lokacin da wani ya karbi wayata."

DAISY:

"Darasin farko, ki yi amfani da kudin soyayya ki sayi kayan abinci, babu wanda zai karba daga baya."

Budurwa Ta Nuna Kyautar Da Saurayinta Ya Mata Tsawon Shekaru 11, Bidiyon Ya Yadu

Kara karanta wannan

Matashi Ya Yi Gadar Katako Akan Kwalbati Don Masu Babura, Ya Tara Kudade

A wani labarin, wata budurwa ta girgiza intanet yayin ta ce saurayinta ya cika mako bai tsinana mata komai ba.

Budurwar ta ce saurayin ba abin da ya taba siya mata sai buroshin goge baki da safa sai kuma man kai, a shekaru 11.

Budurwar ta fusata inda ta mayar masa da dukkan wadannan abubuwa uku da ya siya mata tsawon shekaru 11.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.