'Yafi 'Yahoo' 'Yahoo': Matashi Ya Yi Gadar Katako Akan Kwalbati Don Masu Babura Su Tsallaka, Bidiyon Ya Yadu

'Yafi 'Yahoo' 'Yahoo': Matashi Ya Yi Gadar Katako Akan Kwalbati Don Masu Babura Su Tsallaka, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani matashi ya samo hanyar samun kudi yayin ya yi karamar matakala akan kwalbati don masu babura su tsallaka
  • A wani faifan bidiyo, an gano masu babura nata kokawa da kuma biyan kudi don tsallake kwalbatin mai cike da ruwa
  • Mutane da dama sun mai da martani akan bidiyon inda suka yabi matashin da cewa hakan da yake yi yafi 'Yahoo' 'Yahoo'

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mutum ya daura karamin katako akan kwalbati ga masu babura don karbar kudade idan sun tsallaka.

A wani faifan bidiyo da @Rivaldo_os10 ya wallafa, an gano masu babura sun yi layi don samun tsallake 'yar karamar gadar.

Matashi ya yi matakalar katako akan kwalbati don masu babura suna tsallakawa
Yadda Matashi Ya Tara Kudade Saboda Matakalar Katako Akan Kwalbati Don Masu Babura. Hoto: Twitter/Rivaldo_os10 and @congotopmode.
Asali: Twitter

A karkashin kwalbatin akwai ruwa, amma babu wanda yasan dalilin da yasa masu baburan suka zabi bin ta wannar hanyar, cewar Legit.ng.

Kara karanta wannan

Diyar Biloniya, Hauwa Indimi, Ta Koka Bayan Ta Siya Tumatir Din N8,000, Jama'a Sun Yi Martani

Masu babura sun cika wurin don tsallake matakalar

Wurin ya kasance kamar kasuwa inda masu babura ke kokawar tsallakawa don ba shi kudi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane da dama sun yi martani inda suka ce hakan yafi ya je yana damfara ta intanet 'Yahoo Yahoo'.

Har zuwa yanzu ba a san inda aka nadi faifan bidiyon ba.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Mutane sun tofa albarkacin bakinsu:

@Uncle_Nazeer:

"Hakan yafi yahoo yahoo."

@Ayour133:

"Zai samu kudi fiye da lauya da ma'aikacin banki."

@Uz_1egbo:

"Samar da mafita."

@AnnieAbiola:

"Allah ya taimaki nemanka."

@adaugo_opara:

"Ba zan taba tsallaka wannan gadar da babur ba, zan sauko kasa na tsallaka, idan ta karye fa?"

@fisayo_tade:

"Yanzu za su mai dashi gasa."

@Danielbabatun18:

"Ka nemo matsala ka kawo mafita yana dai-dai da samun kudi."

@t_plarge:

Kara karanta wannan

“Ta Yi Kama Da Shi”: Tsohuwa Da Ta Yi Kama Da Shugaban Kasa Bola Tinubu Ta Yadu a TikTok

"Abin dariya, yana taimakon mutane ne."

'Bana So': Mai Gida Ya Gargadi Mai Haya Da Ya Bar Kula Matarsa Ko Ya Fuskanci Kora

A wani labarin, mai gida ya yi barazanar korar mai haya a gidansa saboda gaishe da matarsa.

Mai gidan ya ce ya lura matar tana son mai hayan ganin yadda suke gaisawa kullum.

Ya gindaya masa sharuda da cewa idan bai fita sha'anin matarsa ba zai kore shi a gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel