"Ba Haka Aka So Ba": Tabo Ya Bata Kwalliyar Amarya a Ranar Biki, Hotunan Sun Yadu

"Ba Haka Aka So Ba": Tabo Ya Bata Kwalliyar Amarya a Ranar Biki, Hotunan Sun Yadu

  • Ruwan saman da aka tafka kamar da bakin ƙwarya bai hana wasu masoya cin moriyar ranar aurensu ba inda aka ɗaura musu aure duk da ruwan da ake yi
  • Ma'auratan an ɗauke su hoto da kayan jikinsu kusan zuwa guiwa duk sun ɓaci da taɓo a wajen bikinsu a yankin Nandi
  • Duk da yanayin da ake ciki, hakan bai sanya murmushi ya ƙi fitowa ba a fuskar ma'auratan yayin da ake ɗaukarsu hotuna domin tarihi

Wasu sabbin ma'aurata sun sosa zukatan mutane da dama bayan hotunansu jiƙe da ruwa a wajen bikinsu sun yaɗu.

Tabo ya bata kwalliyar amarya a ranar biki
Duk da bacin da kayansu suka yi, ma'auratan sun yi hotuna cike da murmushi Hoto: Alfred Koech -Sergent.
Asali: Facebook

An sha biki cikin taɓo

A cikin hotunan da aka sanya a Facebook, amaryar Judith Kisang da mijinta, Abu Robby sun yi hoto tare da Emgwen MP Josses Kiptoo Kosgey a cikin wani fili cike da taɓo, sannan tufafinsu duk ya gama birkiɗa a cikin taɓo.

Kara karanta wannan

"Ba Sauki a Kasar Nan": Ango Ya Bata Rai Lokacin Da Matarsa Ta Daukesu Tare, Bidiyon Ya Yadu a TikTok

Ma'auratan dai ba a daɗe da ɗaura musu aure ba inda basu bari ruwan da ake yi ba ya sanya sun ƙi yin murnar wannan muhimmiyar ranar a wajensu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sabbin ma'auratan suna cike da farin ciki yayin da suke ta ɗaukar hotunansu a cikin taɓon domin tarihi.

Alfred Koech -Sergent shi ne ya sanya hotunan a Facebook inda ya rubuta:

"Nandi tumebarikiwa an sha ruwa kamar da bakin ƙwarya. Ina taya ku murnar aurenku. Ko taɓo basu bari ya rabasu ba. Muna mu ku fatan alkhairi."

Mutane da dama sun yaba wa sabbin ma'auratan

Blacamerican Cheptum Caro ta rubuta:

"Komai wuya komai rintsi, zan kasance da kai masoyi."

Claire Kibet ta rubuta:

"Har ya tunamin da auren taɓo-taɓo... Fatan farin ciki ga sabbin ma'auratan."

Dismas Kibungei Dc ya rubuta:

Kara karanta wannan

Bello Turji Ya Sako Mutum 20 Da Yaransa Suka Yi Garkuwa Da Su, An Bayyana Dalili 1 Da Yasa Yayi Hakan

"Ƙauna ta yi nasara kamar ko da yaushe. Fatan aurenku ya yi albarka."

Kipronoh Munishi ya rubuta:

"Fatan alkhairi. Hata kwa mvua na kiangazi watakuwa pamoja."

Ango Ya Bata Bayan Daura Masa Aure Da Amaryarsa

A wani labarin na daban kuma, wani ango ya shiga cikin duniyar tunani jim kaɗan bayan an ɗaura musu aure da amaryarsa.

Angon dai ya haɗe rai kamar wanda ba ya farin ciki da auren nasa, yayin da amarya kuwa ta ke ta shan waƙarta cike da farin ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng