"Abubuwa Sun Yi Tsada": Ango Ya Bata Rai Lokacin Da Matarsa Ta Daukesu Tare, Bidiyon Ya Yadu a TikTok

"Abubuwa Sun Yi Tsada": Ango Ya Bata Rai Lokacin Da Matarsa Ta Daukesu Tare, Bidiyon Ya Yadu a TikTok

  • Bidiyon wani ango wanda yake cikin bacin rai lokacin da amaryarsa ta ɗaukesu a cikin mota ya yaɗu sosai a TikTok
  • Amaryar na ta rera waƙarta cikin shauƙi yayin da angon ya rasa abinda yake masa daɗi yayin da tsunduma cikin kogin tunani
  • Mutane da dama sun yi tunanin cewa ko halin tsadar rayuwar da ake ciki ya sanya ya fara tunanin ko ya ɗaukowa kansa babban aiki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani bidiyo da ke nuna wani ango ransa a ɓace yayin da amaryarsa ta ke ɗaukarsu a cikin mota ya ɗauki hankulan mutane sosai a TikTok.

Amaryar na ta rera waƙarta cikin farin ciki da shauƙi yayin da angon ya ɓata rai inda ya tsunduma cikin tunani kamar wani abu na damunsa.

Ango ya bata rai lokacin da amarya ke musu bidiyo
Angon ya bata rai a ranar bikinsu Hoto: @agba_monie
Asali: TikTok

Bidoyon angon da ya ɓata rai bayan ɗaurin aure ya yaɗu

Kara karanta wannan

"Ba Zan Amsa Ba Sai Kin Duƙa Kan Guiwa" Bidiyon Yadda Wani Magidanci Ya Ƙi Karban Abinci Daga Matarsa Ya Ja Hankali

Mutane da dama da suka kalli bidiyon, sun yi tunanin cewa ko halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki ne a Najeriya yanzu ya sanya ya fara dana sanin auren da ya yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin bidiyon, an nuna amaryar na bin wata waƙar Hausa tana ɗan takawa, yayin da angon ya kalli gefen tagar motar ransa a ɓace.

Bai damu da abinda matarsa ta ke yi ba wanda a bayyane ya nuna tana cikin nishaɗi.

Wasu daga cikin mutanen da suka kalli bidiyon ya sanya su raha sannan sun yabawa amaryar kan ƙwarin guiwar da ta nuna. Sun kuma yaba da kyawunta.

Sai dai, wasu daga ciki sun nuna damuwarsu kan halin da angon yake ciki inda suka yi tunanin cewa an ya kuwa yana farin ciki da auren nan.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Waliyyin Amarya Ya Sace Sadakin Amarya Ana Shirin Daura Aure a Masallaci

Sun yi tunanin cewa ƙila ya gaji ne ko kuma hankalinsa ya tashi ne saboda halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki a Najeriya, wanda ya ƙara taɓarɓarewa a cikin ƴan shekarun nan.

Wasu sun yi tunanin cewa ya fara dana sanin auren da ya yi saboda ɗumbin ɗawainiyar da ke a cikinsa.

Taron Biki Ya Watse Bayan Amarya Ta Gano Wani Sirrin Ango

A wani labarin kuma, wani taron biki ya tarwatse bayan amarya ta wani sirrin ango da ya daɗe yana ɓoye mata.

Amaryar dai ta gano ashe angon yana da ƴaƴa bakwai da wata matar waɗanda bata san da su ba, nan da taron biki ya tarwatse.

Asali: Legit.ng

Online view pixel