"Ku Zo Ku Auri 'Ya'Yana Suna Da Kyau": Wata Mata Ta Koma Tallar Yaranta Mata, Tace Sun Dade Ba Miji

"Ku Zo Ku Auri 'Ya'Yana Suna Da Kyau": Wata Mata Ta Koma Tallar Yaranta Mata, Tace Sun Dade Ba Miji

  • Bdiyon wata mahaifiya tana gayyatar samari su zo su auri ƴaƴanta ya yaɗu a Instagram inda aka yi ta mahawara a kansa
  • A cikin bidiyon, matar ta bayyana cewa ƴaƴanta har sun wuce lokacin ganiyarsu inda tace suna buƙatar natsatstsen abokin rayuwa
  • Ta kuma buƙaci iyaye maza da su sanya ƴaƴansu su yi aure ta yadda za su auri ɗaya cikin ƴaƴanta domin sun daɗe ba miji

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani bidiyon ban dariya na wata mahaifiya wacce ke nemawa ƴaƴanta mata mazajen aure ya ɗauki hankulan mutane sosai a manhajar Instagram.

A cikin bidiyon, matar ta yi bayanin cewa ƴaƴan nata kullum ƙara tsufa su ke yi sannan suna buƙatar su samu abokan rayuwa ba tare da ɓata lokaci ba.

Wata mata ta koma neman mazajen aure ga kyawawan 'ya'yanta
Matar tace sun daɗe ba miji Hoto: @realtalkauntyf
Asali: Instagram

Bidiyon wata mata mai gayyatar samari su auri ƴaƴanta ya yaɗu

Kara karanta wannan

"Ba Sauki a Kasar Nan": Ango Ya Bata Rai Lokacin Da Matarsa Ta Daukesu Tare, Bidiyon Ya Yadu a TikTok

Ta kuma roƙi sauran iyaye maza da su ƙarfafi guiwoyin ƴaƴansu su zo su nemi aure daga cikin ƴaƴanta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasu daga cikin waɗanda suka kalli bidiyon sun yi masa kallon abin raha inda suka yabawa matar kan halin barkwancin da ta nuna da kuma gaskiyarta.

Bidiyon yana ɗaya daga cikin bidiyoyin da suka yaɗu sosai a Instagram waɗanda aka yi ta tafka mahawara a kansu.

Ga kaɗan daga cikin sharhin da aka yi akan bidiyon:

@dcrypto.kings ya rubita: "

"Ki fara tambayar ƴaƴanki idan suna da hankali tukunna."

@iamcy_rodriguez ya rubuta:

"A shirye na ke."

@harryboygram:

"Anty daga cikin ƴaƴan na ki waccece ta ke a kasuwa yanzu?"

@ajebutter_putin ya rubuta:

"Mama matsalar ba daga wajen samari ba ne, ƴan matan nan basu shirya ba sam, ba sa son matasan da suka dage wajen neman na kansu, sun fi son ƴan Yahoo da ƴan damfara waɗanda za su kai su manyan birane yawon shaƙatawa. Su ma iyaye da na su laifin inda su ke tsawwalawa wajen kuɗin sadaki da siye-siye na rashin kan gado."

Kara karanta wannan

Bello Turji Ya Sako Mutum 20 Da Yaransa Suka Yi Garkuwa Da Su, An Bayyana Dalili 1 Da Yasa Yayi Hakan

Budurwa Ta Koka Bayan An Fasa Aurenta

A wani labarin kuma wata budurwa ta shiga damuwa bayan an fara aurenta ana saura sati biyu kacal a ɗaura musu aure da saurayinta.

Budurwar wacce ke ɗauke da juna biyu ta bayyana cewa ƴan katsalandan ne suka shiga suka fita har sai da aka fasa bikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng