An Maka 'Group Admin' A Kotu Kan Zargin Cire Mamba A Rukunin 'WhatsApp', Ya Samu Karin Girma

An Maka 'Group Admin' A Kotu Kan Zargin Cire Mamba A Rukunin 'WhatsApp', Ya Samu Karin Girma

  • Wani mutum mai suna Herbert Baitwababo ya maka mai gudanar da rukunin manhajar 'WhatsApp' a kotu
  • Herbert ya ce ya maka Allan a kotu ne bisa zargin cire shi a 'WhatsApp' bayan ya biya kudin rijistar zama mamba
  • Kotun ta umarci Allan ya mayar da Herbert rukunin tare da ba shi matsayin mai gudanarwa a rukunin shi ma

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mutum mai suna Herbert Baitwababo ya maka mai gudanar da rukuni a manhajar 'Whatsapp' saboda ya cire shi a rukuni, cewar Legit.ng.

Herbert ya bayyana wa kotu a ranar 16 ga watan Mayu cewa ya rubuta takarda zuwa ga shugaban gudanarwa na rukunin, Allan Asinguza don neman a binciki yadda ake kashe kudade a rukunin tun bayan kirkirarta a 2017.

Wani ya maka 'Group Admin' a kotun kan cire shi a 'WhatsApp'
Matashin Da Ya Maka 'Group Admin' A Kotu. Hoto: Guiding Tech, Twitter/@IamMzilikazi.
Asali: Twitter

Herbert ya shigar da karar a wata kotun magistare da ke zamanta a birnin Kampala da ke Uganda, cewar rahotanni.

Kara karanta wannan

Yadda Magidanci Ya Kange Matarsa Tare Da Hana Ta Abinci Na Tsawon Shekaru Biyu a Wata Jihar Arewa

Herbert ya kai kara kotu ne don bin kadunsa akan cire a 'WhatsApp'

Rukunin 'Whatsapp' din mai suna "Buyanja My Roots" don taimakon al'umma da kuma yin jaje ga mutane.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce an bude rukunin ne don taimakawa kuma kowa yana ba da gudumawar kudi da kuma kudin rijistar zama mamba.

Alkalin rikon kwarya na kotun, Igga Agiru a ranar Litinin 19 ga watan Yuni ya ba da umarnin dawo da Herbert cikin rukunin.

Kotun har ila yau, ta hana mai gudanar da rukunin da mukarrabansa da kada su sake take hakkin Herbert tun da akwai 'yancin taro a kundin tsarin mulki.

An dawo da Herbert cikin rukunin da kara masa girma

Abin mamaki, an dawo da Herbert wanda aka kara masa girma zuwa mai gudanar da rukunin, yayin da sauran mambobin suka rinka fita daya bayan daya.

Kara karanta wannan

"Ina Kaunar Mijina Duk da Yana Bugu Na Kamar Jaka" Wata Mata Ta Nemi Saki a Kotun Musulunci, Ta Gindaya Sharaɗi 1

Wani dan jarida, Mzilikazi ya tabbatar da cewa Herbert ya sake dunguma kotu don dawo da sauran mambobin.

Mzilikazi ya wallafa faifan bidiyo kan lamarin.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu.

khumaloMel:

"Ina tunanin kawai zance ake a rukunin, amma rukunin harkar kasuwanci kuma na gaske daban ne, ina tunani.... "

@tebogoyannete:

"Babu abinda yakai cire mutum a rukuni haushi ko da rukunin ba shi da amfani."

@charles_jjuuko:

"Hehehe ....na ji an dawo da shi kuma sauran mambobi suna fita don kirkirar wani rukuni."

@naijama:

"A bayyane, kowa zai biya kafin kasancewa cikin rukunin kuma ya biya, ina tsammanin wannan daban ne da sauran rukunin manhajar 'Whatsapp'."

Makaho Da Ke Amfani Da Wayar ‘IPhone’ Kamar Sauran Mutane, Ya Girgiza Intanet

A wani labarin, wani makaho mai suna Waziri Ahmed ya bayyana yadda ya ke amfani wayar 'IPhone'.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tasa Keyar Matashi Mai Shekaru 18 Zuwa Gidan Dan Kande Kan Zargin Satar Akuya, Ya Samu Rangwame

Waziri ya bayyana yadda abin ya faru da shi da cewa yana cikin tuki ya hadu da 'yan fashi.

'Yan fashin sun bukaci ya ba su wayarsa tare da harbinshi a fuska wanda ya yi sanadin rasa idanunsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.