"Ta Ki Yarda Ta Tsufa": Hotunan Wata Mata Mai 'Ya'Ya 7 Da Jikoki 5 Sun Janyo Cece-Kuce a Intanet

"Ta Ki Yarda Ta Tsufa": Hotunan Wata Mata Mai 'Ya'Ya 7 Da Jikoki 5 Sun Janyo Cece-Kuce a Intanet

  • Wata mata ƴar Najeriya mai kama da matashiya ta bayar da mamaki sosai a yanar gizo bayan hotunanta sun bayyana
  • Kyakkyawar matar wacce ta ke da ƴaƴa bakwai da jikoki biyar ta ba masu amfani da yanar gizo mamaki saboda yanayin halittarta
  • Masu amfani da Soshiyal Midiya sun bayyana ra'ayoyinsu akan bidiyon inda da yawa daga cikinsu suka riƙa fatan su zama kamarta bayan sun haihu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata budurwa mai amfani da sunan @soh_marrh a manhajar TikTok ta yaɗu a Soshiyal Midiya bayan ta sanya hotunan mahaifiyarta wacce ba ta tsufa ba.

Budurwar wacce ta rubuta a jikin hoton cewa "Na shiga gasar, ku haɗu da mahaifiyata wacce ba ta tsufa ba," ta sanya kyawawan hotunan mahaifiyarta wacce alamu suka nuna shekarunta maimaikon su yi gaba sai suka yi baya.

Kara karanta wannan

“Kina Karawa Addinin Musulunci Kyau”: Jaruma Mercy Aigbe Ta Nunawa Duniya Mijinta Yayin da Suke Aikin Hajji

Dattijuwa mai kama da budurwa ta ɗauki hankula
Kyawunta na nan daram kamar na budurwa Hoto: @soh_marrh/TikTok.
Asali: TikTok

Duk da cewa tana da ƴaƴa bakwai da jikoki biyar, matar har yanzu da sauran jini a jikinta inda idan ba a ankare sosai ba za a iya tunanin cewa sabuwar amarya ce.

Wallafar da budurwar ta yi dai ta janyo cece-kuce a Soshiyal Midiya inda mutane da dama suka riƙa yabawa da kyawunta da kama da ta ke yi da matashiyar budurwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kyakkyawar matar dai ta ɗauki hotuna cikin kaya daban-daban waɗanda suka yi mata kyau sosai suka ƙara bayyana kamanninta da na budurwa.

Ra'ayoyi yayin da hotunan mata mai ƴaƴa 7 suka bayyana

@appleuser638552441 ya rubuta:

"Kamar mahaifiyata waɗannan matan nan basu son tsufa."

@Ruby_Ikwen ta rubuta:

“Shin wannan ƙanwarki ce?"

@Okafor Chioma ta rubuta:

"Shekarunta baya su ke komawa."

@Krystal ta rubuta:

"Kyakkyawar mata."

@Sandy ta rubuta:

Kara karanta wannan

“Uwar Miji Ta Ce Ba Zan Taba Haihuwa Ba”: Yar Najeriya Ta Samu Cikin Yan 3, Ta Nuna Wa Duniya

"Mahaifiyarki ta fi ni rashin tsufa."

@user9074433896038 ya rubuta:

"Idan na haɗu da ita a hanya kuma ban sani ba, ki yi haƙuri da budurwa zan kirata."

@Chioma Akoma ya rubuta:

"Wai kina nufin wannan ba ƙanwarki ba ce?"

@Joy Ozi ta rubuta:

"Ba hoton mahaifiyarki kika sanya ba. Muna jiran mu ganta."

@bellofaiza500 ta rubuta:

"Tabbas lallai ba ta tsufa."

@Goodness Zeno ya rubuta:

"Mahaifiyarki ko ƙanwarki?"

Budurwa Ta Ginawa Mahaifiyarta Katafaren Gida

A wani labarin kuma, wata budurwa ta yi abin a zo a gani shekara ɗaya bayan ta bar ƙasarta ta yi hijira zuwa ƙasar waje neman na abinci.

Budurwar wacce ke aikin koyarwa a ƙasar Koriya ta turo kuɗi an ginawa mahaifiyarta katafaren gida domin ta shiga ta wala ta ji daɗinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng