Na Yi Nadamar Auren Mijina, In Ji Jarumar Najeriya Ini Edo

Na Yi Nadamar Auren Mijina, In Ji Jarumar Najeriya Ini Edo

  • Shahararriyar 'yan wasan kwaikwayo ta Nollywood, Ini Edo ta bayyana irin kalubalen da ta fuskanta a dakin mijinta
  • Ini Edo ta bayyana haka ne yayin wata hira da dan jarida Chude Jideonwo inda ta ce auren dole iyayenta suka yi mata
  • Ta ce zai yi wahala ta sake yin aure a rayuwarta saboda matsalolin da ta fuskanta a lokacin da take zaman aure

'Yar wasan kwaikwayo ta Nollywood, Ini Edo ta bayyana yadda aurenta ya samu tasgaro yayin wata hira da dan jarida Chude Jideonwo.

Ta ce zai yi wahala ta sake yin aure a rayuwarta saboda irin matsalolin da ta fuskanta yayin zaman aure.

Ba zan sake yin aure ba kuma na yi dana sani, Ini Edo
Shahararriyar 'Yar Wasan Kwaikwayo Na Nollywood, Ini Edo. Hoto: allAfrica.com.
Asali: Facebook

A ranar 30 ga watan Nuwamba ta shekarar 2008, Ini Edo ta auri wani dan kasuwa da ke zama a Amurka, Philip Ehiagwina, cewar Punch.

Kara karanta wannan

“Ya Fi Kudin Jini”: Budurwa Ta Yarda Ta Mari Mahaifiyarta a Kan Miliyan N2, Ta Ce Mahaifiyar Tata Za Ta Fahimce Ta

Aurenta da Philip ya wargaje bayan shekaru 5 da yin auren, wanda suka rabu a shekarar 2013.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana yadda iyayenta suka mata auren dole

Ta kara da cewa, iyayenta ne suka tilasta mata yin auren, saboda haka taso idan za ta sake aure ta auri wanda ya kwanta mata a rai kuma wanda ya dace.

A cewarta:

"Na yi dana sanin yanke shawarar yin wannan auren, saboda ba abin da ya dace ba ne.

A shekarar 2021, 'yar wasan kwaikwayon ta haifi jariri ta hanyar yin hayar mahaifar wata matar daban don dauka mata cikin, Daily Trust ta tattaro.

Ta bayyana yadda ta haihu

Ta ce tana yawan samun barin ciki, madadin haka sai ta yi amfani da koyayen halittar ta don samun haihuwa wanda wata ta dauki nauyin cikin.

Kara karanta wannan

"Bayan Wuya": Matashiya Wacce Ke Yawon Talla Ta Koma Turai, Ta Fara Aiki a Matsayin Malamar Asibiti

Ta kara da cewa:

"Bani da miji amma ina son haihuwa, na ji inason yaro na kaina ko inada miji ko babu. Bani da wani zabi, kuma ina son ya zama yaro na, koyaye na, madalla da samun koyaye na masu kyau, hakan na yi."

Ayyuka Da Suka Yi Min Yawa Ne Ya Hana Ni Shiga Jirgin Da Ya Gamu Da 'Bala'i, Ned Nwoko

A wani labarin, dan siyasa Ned Nwoko ya bayyana yadda bai samu shiga jirgin ruwan da ya kife ba saboda ayyuka.

Nwoko ya ce marigayi Hamish Harding ya gayyace shi zuwa ziyarar buraguzan jirgin ruwan Titanic amma bai samu halarta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.