"Ba Zan Maimaita Darasin Yau Ba": Bidiyo Ya Nuna Lakcara Shi Kadai a Aji Dalibai Sun Ki Zuwa

"Ba Zan Maimaita Darasin Yau Ba": Bidiyo Ya Nuna Lakcara Shi Kadai a Aji Dalibai Sun Ki Zuwa

  • Wani bidiyo ya nuna wani lakcara yana ta surutu a cikin wani aji wanda babu ɗalibi ko ɗaya a ciki duk da an koma makaranta
  • A cikin bidiyon wanda aka sanya a Twitter, lakcaran ya tsaya kamar yana a gaban ɗalibai sannan ya riƙa koro bayanansa
  • Lakcaran ya yi gargaɗin cewa ba zai maimaita karatun da yakamata ya yi ba a ranar idan ɗaliban suka dawo makaranta

Wani bidiyo da ya yaɗu ya nuna wani lakacara yana ta zabga surutu shi kaɗai a cikin aji babu kowa a tare da shi.

Lakcaran dai yana koyarwa ne a wata kwalejin fasaha amma sai dai ba a bayyana sunan makarantar ba da kuma a inda ta ke.

Lakcara ya koyar a ajin da babu dalibai
Lakcaran ya ce ba zai maimaita darajin ranar ba Hoto: Twitter/@FrankTalkNow1
Asali: Twitter

A cikin bidiyon, lakcaran yana tsaye a cikin ɗakin karatun inda yake ta surutu kamar yana a gaban ɗalibansa.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Yi Martani Mai Zafi Ga Wike Bisa Ikirarin Cewa An Sanya Masa Guba a Sakatariyar PDP

Bidiyo ya nuna lakcara shi kaɗai a cikin aji

Ɗaliban dai sun ƙi zuwa aji ne duk kuwa da cewa an dawo hutun makaranta domin ci gaba da karatu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai lakcaran bai damu ba, inda ya gabatar da jawabin sharar fage ba tare da ya fasa ba.

Ya kuma yi gargaɗin cewa ba zai dawo ya sake koyar da darasin ba lokacin da ɗaliban suka ga dama suka zo aji.

A kalamansa:

"Jiya mu ka dawo hutu sannan an buɗe makaranta. Wannan wani aji ne wanda zan koyar. Ajin ƴan HNDII ne public administration. Ina son tabbatar mu ku da cewa ba zan maimaita darasin yau ba idan kun dawo."

Bidiyon dai wani amfani da sunan @FrankTalkNow1 ne ya sanya shi manhajar ta Twitter.

Ku kalli bidiyon nan ƙasa:

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Matar Da Ta Farfado Ana Shirin Kaita Makwanci Ta Sheka Da Gaske

Lakcara Ya RokI Dalibai Su Dawo Makaranta

A wani labarin na daban kuma, wani lakcara ya koma magiya da roƙo ga ɗalibansa domin su daure su dawo makaranta a ɗora daga inda aka tsaya a fannin karatu.

Lakcaran dai ya roƙi ɗaliban da su daure su cije su samu abinda suka sami su dawo makaranta su ci gaba da ɗaukar karatu kamar yadda aka saba.

Ya bayyana cewa ya san abubuwa sun yi wuya amma a hakan za su daure su dawo makaranra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng