Babu Macen Da Za Ta Ciyar Da Gida Na Wata 1 Ba Tare Da Cin Zarafin Miji Ba, Bidiyon Ya Yadu
- Budurwa ta jawo cece-kuce inda ta wallafa wani faifan bidiyo a TikTok da ya burge mutane
- Budurwar ta ce babu macen da ke ciyar da iyalinta har na wata daya ba tare da cin mutuncin miji ba
- Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu inda wasu suka ce ai wata daya ma ya yi yawa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata budurwa ta burge mutane da dama bayan bayyana yadda mata suke musamman masu ciyar da iyalansu.
A wani faifan bidiyo, budurwa mai suna Claire-Wiyfengla ta ce yana iya yiyuwa mata tana yawan cin zarafin mjijnta musamman idan ita take ciyar da shi.
Ta ce duk yadda mace take da kan-kan da kai, zai yi wahala ba ta ci mutuncin mijinta ba ko sau daya kafin wata ta kare.
A cewarta:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Duk yadda mace take da saukin kai da kuma mutunta mijinta, ba za ta iya ciyar da iyalinya na wata daya ba, ba tare da taci zarafin mijinta ba."
Kalli bidiyon Claire a kasa:
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu musamman mutanen da suka ji dadin abin da ta fada.
Wasu da dama sun ce wata daya ma ya yi yawa idan dai mata take ciyar da iyali dole ba za ta jure ba sai ta ci mutuncin mijinta, cewar Legit.ng.
Martanin mutane masu ta'ammali da sada zumunta:
@user3875773211874:
"A gaskiya, ko dubu daya mace ta cika akan dubu 10 da mijinta ya bayar kadai ya isa ya sa mata ta ci mutuncin mijinta."
@Ramsey:
"Kai ki kai har wata daya, mako daya kadai idan miji bai saka komai ba, ya shiga iku."
@Tate Namholo:
"Makwanni biyu kadai ya isa, kafin sarauniya ta fara nuna isarta a gidan, ina magana akan matana."
@Kallin:
"Ya kamata a baki kariya."
@TopeBabs:
"Mako daya ya yi kadan, kafin ta fara kiranka da sunan haihuwarka madadin 'Baby' a cikin murya marar dadi."
"Ya Yi Bulokin Dina": Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Dandana Abincinta Ya Tsere
A wani labarin, wata budurwa ta koka kan yadda saurayinta ya gudu bayan dandana abincin da ta girka masa.
Budurwar ta ce a halin yanzu ko wayanta ba ya dagawa kuma ba ta san dalilin yanke wannan hukunci ba.
Asali: Legit.ng