"Duk Su Na Masifar Ƙaunata": Matashi Mai 'Yan Mata Biyu Ya Rasa Ta Zaba, Ya Koma Neman Taimako

"Duk Su Na Masifar Ƙaunata": Matashi Mai 'Yan Mata Biyu Ya Rasa Ta Zaba, Ya Koma Neman Taimako

  • Wani matashi ɗan Najeriya mai ƴan mata guda biyu ya koka a soshiyal midiya kan yadda ya kasa zaɓar guda ɗaya daga cikinsu
  • A cewarsa, yana da ƴan mata guda biyu waɗanda su ke masifar son shi amma ya yanke shawarar guda ɗaya kawai zai zaɓa
  • Matashin wanda ya rasa abin yi ya bayyana halayen da kowace daga cikin ƴan matan nasa ta ke da su

Wani matashin saurayi ya janyo cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya nemi da a taimaka masa da shawara kan halin ƙaƙaniƙayin da ya samu kansa a ciki.

Matashin mai suna Itz Bleszo YoungArtist, a wata wallafa da ya yi a Facebook, ya nemi shawarar da a taimaka masa kan matsalar da yake fuskanta.

Matashi ya nemi shawarar budurwar da yakamata ya zaba cikin 'yan matansa
Matashin ya nemi da a ba shi shawarar wacce zai zaba Hoto: RicardoImagen/ Getty images.
Asali: Getty Images

A cewarsa yanzu haka yana soyayya da ƴan mata guda biyu waɗanda duk suna masifar ƙaunar shi, sannan ya kasa zaɓar guda ɗaya daga cikinsu.

Kara karanta wannan

"Wannan Bata Da Kunya": Hirar Wata Budurwa Da Wani Saurayi Ta Janyo Mahawara a Yanar Gizo

A cikin wallafar da ya yi, Itz Bleszo ya bayyana halayen da kowace daga cikin ƴan matan nasa ta ke da su, da illa da kuma amfanin kasancewa da kowace daga cikinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana halayen kowacce daga ciki

Ya yi bayanin cewa ta farko daga cikinsu mai taimako ce, ga kula kuma tana da jajircewa wajen neman na kanta amma tana da saurin fushi da daɗewa kafin ta yi yafiya.

Ta biyun kuma bata fara aiki ba amma tana da kula, biyayya sannan tana da shiri mai kyau kan gobenta.

Itz Bleszo ya buƙaci mabiyansa da su ba shi shawarar wacce zai ɗauka daga cikinsu, musamman waɗanda suka taɓa tsintar kansu a halin da ya samu kansa a ciki.

A kalamansa:

"Ina da ƴan mata guda biyu waɗanda na ke soyayya da su yanzu haka. Dukkansu suna masifar sona, amma ina ƙokarin ganin na yi zaɓi mai kyau. Wacce yakamata ace na zaɓa daga cikinsu?"

Kara karanta wannan

"Har Lakada Min Duka Ta Taba Yi": Magidanci Ya Garzaya Kotu Neman a Korar Masa Tsohuwar Matarsa Daga Gida

Nan da nan rubutun nasa ya yaɗu, inda mutane da dama suka yi ta bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin.

Wasu sun shawarci Itz Bleszo da ya zaɓi wacce ta ke da taimako da ƙwazo wajen neman na kanta, yayin da wasu kuma suka ba shi shawarar ya mayar da hankali kan mai yi masa biyayya da kulawa.

Matashi Ya Koka Bayan Ya Hadu Da Budurwa Mai Son Abun Duniya

A wani labarin wani matashi ya sanya hirar da suka yi da wata budurwa wacce ya nuna alamar yana so a yanar gizo.

Bayan gabatar da buƙatarsa da neman lambar wayarta, budurwa ta nemi da sai ya kashe mata kuɗaɗe kafin ta yi na'am da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng