Hilda Baci: Abu 6 Da Mutum Zai Amfana Da Su Bayan Kafa Tarihi A Kundin Bajinta Na Guinness

Hilda Baci: Abu 6 Da Mutum Zai Amfana Da Su Bayan Kafa Tarihi A Kundin Bajinta Na Guinness

  • Hilda Baci ta kafa tarihi bayan da ta shafe sa'o'i akalla 100 tana girki don zama wadda ta fi kowa dadewa ta na girki
  • Hilda ta yi kokarin ganin ta kafa tarihi don shafe sa'o'i 100 tana girki, amma hakan bata samu ba yayin da ta kwashe sa'o'i 93
  • Mutane da dama suna kokwanton shin akwai wani amfani da kafa wannan tarihi ke da shi tun da ba kudi a ke bayarwa ba?

Kundin Bajinta na Guinness ya ayyana Hilda Baci a matsayin wacce ta kafa tarihi bayan ta shafe sa'o'i ta na girki.

Ta yi kokarin ganin ta cika sa'o'i 100 ta na girki amma an samu gibin sa'o'i 7 saboda ta yi amfani da lokacin wurin wutawa.

Hilda Baci ta kafa tarihi a matsayin wacce ta fi kowa dadewa ta na girki
Hilda Baci Ta Kafa Tarihi Na Guiness World Record. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Talata 13 ga watan Yuni ya ce:

Kara karanta wannan

"Sai Da Ya Yi Hawaye": Matashiya Ta Ba Direba Mai Kirki N10,000 Bayan Ya Caje Ta N2,500 Duk Da Tsadar Mai

"Bayan nazari mai zurfi, Guinness World Record ya tabbatar da Hilda Baci a matsayin wacce ta fi kowa dadewa ta na girki cikin sa'o'i 93."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mafi yawan mutanen Najeriya suna tambayar shin akwai wani fa'ida da kafa wannan tarihin? Ganin yadda Hilda ta hana kanta bacci akansa.

Kamfanin ya ce ba ya ba da kudi, amma ya na ba da takardar shaida da kuma darajar jin cewa mutum ya kafa tarihi don samun karfin gwuiwa a gaba, cewar rahotanni.

Bayan takarar shaida, Daily Trust ta jero wasu alfanu dangane da kafa wannan tarihin.

1. Sanuwa a duniya

Daga cikin amfanin wannan kafa tarihi akwai sanuwa da mutum zai yi a duniya a dalilin wannan tarihi, mutane za su san mutum a duk inda ya ke tunda abu ne da ya shafi duniya baki daya.

Kara karanta wannan

"Ta Kwashe 'Ya'yana Ta Tafi Da Su": Magidanci Ya Koka Bayan Matarsa Da Suka Dade Ta Rabu Da Shi

2. Daraja ta musamman ga wanda ya kafa tarihin

Duk wanda ya kafa wannan tarihi to zai samu wata daukaka ta musamman a karan kansa, da kuma samun kwarin gwuiwar cewa shi kadai ya kafa wannan tarihin.

3. Kwarin Gwiwa

Kafa wannan tarihi zai karawa wadanda ba su shiga gasar ba kwarin gwuiwa don ganin suma sun samu wannan damar ta zamtowa zakara a wani bangare na rayuwarsu.

4. Tallace-tallace wa kamfanoni

Tabbas samun wannan dama zai sa kamfanoni su bukaci wanda ya kafa wannan tarihi don tallata musu hajarsu wanda a karshe zai tashi da miliyoyin Nairori dalilin tallan.

5. Magana a bainar jama'a da kuma samun kudin shiga

Mafi yawan wadanda suka kafa wannan tarihi ana biyansu don su halarci wani taro ko biki don karrama bikin da kuma kasancewa a hira da gidajen talabijin don biyansu.

6. Siyar da littattafai da kuma kasuwanci

Da dama daga cikin wadanda suka kafa wannan tarihi na samun dama daga kamfanonin don siyar musu da kayayyakinsu wadda suma ke samar musu da makudan kudade.

Kara karanta wannan

Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Jami'an Tsaro Suka Mamaye Dakataccen Gwamnan CBN a Filin Jirgin Sama

Abubuwan da Baku Sani Ba Game da Hilda, ’Yar Najeriya Ta Farko da Ta Jera Kwana 4 Tana Girki

A wani labarin, Hilda Baci, budurwa 'yar asalin jihar Akwa Ibom da ke zama a jihar Lagos ta na daf da kafa tarihi.

Budurwar wacce ta dukufa sai ta karya tarihin wacce tafi kowa dadewa ta na girki a duniya.

Guiness World Record ya kasance kamfanin da yake ba wa duk wanda ya yi wani abin bajinta takardar shaida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.