FG Ta Yi Kuskuren Biyan Yar Bautan Kasa N330,000 Maimakon N33,000, Ta Nemi Shawarar Matakin Da Za Ta Dauka

FG Ta Yi Kuskuren Biyan Yar Bautan Kasa N330,000 Maimakon N33,000, Ta Nemi Shawarar Matakin Da Za Ta Dauka

  • Wata matashiya mai bautar kasa a Najeriya ta bayyana yadda Gwamnatin Tarayya ta biya ta kudi N330,000 madadin N33,000
  • A wani faifan bidiyo da ta wallafa, budurwat ta ce an biya ta alawus na wata daya wanda ya kai kusan ninki goma da ya kamata a biya ta
  • A baya Gwamnatin Tarayya na biyan matasa masu bautar kasa N19,800 kafin daga bisani ta kara zuwa N33,000 dalilin biyan mafi karancin albashi

Wata matashiya mai bautar kasa a Najeriya ta bayyana yadda aka biya ta kudin alawus na bautar kasa N333,000 madadin N33,000.

Gwamanatin Tarayya a baya ta kara kudin matasa masu bautar kasa daga N19,800 zuwa N33,000 a lokacin da aka kara mafi karancin albashi.

'Yar bautar kasa ta shirya mayar da kudi N330,000 maimakon N33,000
Matashiya Yar NYSC Ta Nemi Shawarar Yadda Za Ta Mayar Da Kudin Alawus. Hoto: GistReel.
Asali: Facebook

A wani faifan bidiyo da ta wallafa, budurwar ta ce an biya ta kudi na wata daya fiye da yadda ake biyansu a kowane wata wanda akalla ya ninka shi sau goma.

Kara karanta wannan

Kina da Dakika 60: Budurwa Ta Kwashi Kaya Kyauta a Kanti Na Makudan Kudade Fiye da N1m

Budurwar ta nemi shawarar hanyar da za ta bi don mayar da kudin

Cikin faifan bidiyon, kamar yadda The Nation ta tattaro, budurwar na sanye da kayan masu baukar kasa da hula, ta nemi shawari daga mutane akan matakin da ya kamata ta dauka dangane da kudin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta ce ta rasa yadda za ta yi da kudin, ta mayar da su ne ko kuma ta ajiye su a wurinta ko kuma ta yi amfani da kadan daga cikin kudin.

Ta tambaya ko ya kamata ta je banki don mayar da kudin?

Rahotanni sun tattaro cewa budurwar ta tambaya ko akwai wata hanya da ta dace ta bi idan tana son maida kudin ga gwamnati.

Ta na neman shawara ko ya kamata ta je banki ta kai rahoto ko kuma ta je karamar hukumar da take bautar kasa don bayyana musu halin da take ciki.

Kara karanta wannan

"Abin Da Ciwo": Wata Da Ke Saudiyya Ta Yi Kuka Ganin Halin Da Yayanta Ke Ciki Duk Da Tana Turo Kudi Duk Wata

Ba Mu Mu Ka Ba Shi Satifiket Ba – NYSC Ta Jefa Sabon Gwamnan Enugu a Matsala

A wani labarin, Hukumar NYSC ta yi magana kan batun takardar shaidar zababben gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah.

Daraktan Hukumar ta NYSC, Birgediya Janar Y. D Ahmed ya ce hukumar ba ta san inda ‘dan siyasar ya samu takarddar shaidarsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.