"Albashinsa N400k": Budurwa Ta Hakikance Sai Saurayinta Ya Siyo Mata Wayar N345k

"Albashinsa N400k": Budurwa Ta Hakikance Sai Saurayinta Ya Siyo Mata Wayar N345k

  • Wata budurwa ta nemi dole sai saurayinta ya yi amfani da fiye da rabin albashinsa ya siyo mata waya
  • Matashin wanda ya ke samun N400,000 a wata, ya siyo mata wayar da kuɗinta sun kai N120,000, amma sai ta fusata inda ta buƙaci ya rabu da ita na wani ɗan lokaci
  • Matashin sai ya ɓace mata da gani kwata-kwata sannan ya daina ɗaukar wayarta ko mayar mata da amsar saƙonnin ta

Wani matashi ya watsar da budurwarsa cikin kwandon shara bayan ya siyo mata wayar N120k, ta nuna ba ta son ta.

A cikin wani rubutu wanda shafin @Yabaleftonline ya sanya a Twitter, budurwar ta bayyana cewa bayan aukuwar hakan sai kawai saurayin na ta ya share ta.

Saurayi ya rabu da budurwarsa kan wayar N345k
Budurwar tace wayar N345k ta ke so Hoto: Getty Images/Yana Iskayeva, Azmanjaka
Asali: TikTok

Ta bayyana cewa saurayin na ta yana ɗaukar albashin N400,000 a wata, sannan ta buƙaci da ya siyo mata wayar da kuɗinta sun kai N345,000.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Girgiza Bayan Budurwarsa Ta Nemi Ya Kawo N12m Domin Bikin Aurensu, Ya Dauki Mataki Mai Tsauri

Sai dai, saurayin na ta ya siyo mata wayar da kuɗinta sun kai N120,000 wacce ita kuma ta nuna ba ta so. Domin nuna ɓacin ranta, ta ɓuƙaci da ya rabu da ita na wani ɗan lokaci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamanta:

"Yanzu wata huɗu kenan ina ta bibiyarsa. Na rubuta masa saƙonni kusan sau 10 satin da ya wuce. Na kira shi amma baya ɗaukar kirana. Ina son na gaya masa cewa na yafe masa ta yadda za mu ci gaba da soyayyar mu. Ina matuƙar son shi. Na yi kewarsa sannan hakan ya fara taɓa lafiya ta."

Ƴan soshiyal midiya sun yi tsokaci

@IruefiNG ya rubuta:

"Ni damuwa ta shine ina fatan dai ya amshi N120k ɗin sa kafin ya rabu da wannan wacce ba ta san arziƙin ba"

@kingdubie_ ya rubuta:

"Ina alfahari da shi"

Kara karanta wannan

"Dole Sai Yana Samun N3m": Budurwa Mai Samun N3.7m a Wata Ta Bayyana Irin Mijin Da Ta Ke Son Yin Wuff Da Shi

@tochi__ ya rubuta:

"Mata masu irin halin ta sun cancanci abinda aka yi mata. Mutumina bai yi ƙorafi ba. Ya kawai tafi ya bar ta inda ya zaɓi zaman lafiyarsa."

@emmysteven_ ya rubuta:

"Abu mafi muni da zai faru da mutum shine ya fara soyayya da waɗanda ba su da godiya kwata-kwata."

Matashi Ya Fasa Auren Budurwarsa Bayan Ta Nemi Ya Kawo N12m

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya fusata inda ya fasa auren budurwarsa wacce zai aura saboda ta nemi ya kawo maƙudan domin shagalin bikin aurensu.

Wacce zai aura ɗin dai ta nemi ya kawo N12m domin shirya shagalin bikinsu. Hakan ya fusata shi ya ce ya fasa auren ta nemi wani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel