Bidiyon Wani Matashi Dan Najeriya Da Ya Fasa Kwakwa Guda 50 Da Hakoransa Ya Karaɗe Intanet

Bidiyon Wani Matashi Dan Najeriya Da Ya Fasa Kwakwa Guda 50 Da Hakoransa Ya Karaɗe Intanet

  • Bidiyon wani ɗan Najeriya ya bazu a shafukan sada zumunta, bayan ya yi amfani da haƙoransa wajen ɓara kwakwa manya-manya har guda 50
  • Matashin ya bayyana cewa ya yi hakan ne domin ya kafa tarihin da za a bashi kambun 'Guinness World Record'
  • Jama'a sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta, a yayin da wasu ke ganin yayin bajinta, wasu kuma na ganin akasin hakan

Wani matashi ɗan Najeriya ya ɓara ɓawon kwakwa aƙalla guda 50 a bainar jama'a ta hanyar amfani da haƙoransa.

A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a shafin sada zumunta na TikTok, an ga matashin yana ɓare ɓawon kwakwar da baki a yayin da ɗumbin jama'a suka kewaye shi domin ba shi ƙwarin gwiwa.

Matashi dan Najeriya ya fasa kwakwa 50 da hakoransa
Matashi dan Najeriya ya fasa kwakwa 50 da hakoransa. Hoto: @mayorofabk
Asali: TikTok

An kuma hangi wani yana ba shi ruwa lokaci bayan lokaci wanda yake kuskure bakinsa da shi domin ƙara samun kuzari.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tura Wani Dattijo Gidan Yari Saboda Sarrafa Kwandala Da Ficika Zuwa Kayan Ado A Kano

Abokansa ne suke ƙara zuga shi

Shewar da jama'a ke yi na ƙara ba shi kwarin gwiwa kan ya ci gaba, haka nan ma abokansa da ke kusa suna ta ƙara zuga shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Masu amfani da yanar gizo sun tafka muhawara kan faifan bidiyon, a inda suka yi masa fatan samun amincewar masu kula da kundin tarihin na 'Guinness' domin ba shi kambu.

Mutane sun tofa albarkacin bakunansu

Mayorofabk, ya rubuta a shafinsa

"Na gode wa Allah da na yi wannan abu lami lafiya. Daga ƙarshe dai na kafa tarihi. Mutumin da ya fara fasa kwakwa 50 da haƙora," .

Masu amfani da kafofin sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu kamar haka:

@ogastreet ya ce:

"Ina jami'ansu?"

@just_one_empress ta ce:

"Guinness na iya ƙin baka kambun fa."

@kexx10 kuma ya ce:

Kara karanta wannan

"Ta Ciri Tuta": Kyakkyawar Bahaushiya 'Yar Najeriya Ta Zama Soja a Amurka, Bidiyonta Ya Yadu Sosai

"Da fatan ya san cewa Guinness ba sa bayar da kyautar kuɗi ko."

@deanability_ ya ce:

"Wannan karon Guinness zasu haramtawa 'yan Najeriya shiga gasar, kada ka damu."

@Irishpresh ya ce:

"Talauci me sa ka gano abubuwa da yawa. Mutumin fa akwai basira."

@maery125 cewa ta yi:

"Da fatan ya san cewa babu batun bayar da kuɗi a 'Guinness World Record' ko."

Ga dai biyon matashin a ƙasa kamar yadda za ku gansa yana ta faman fasa kwakwar da bakinsa:

'Yar Najeriya ta kafa babban tarihi a duniya

A wani labarin na daban, a kwanakin nan ne dai aka samu wata 'yar Najeriya mai suna Hilda Baci da ta kafa tarihi a duniya, ta hanyar shafe sama da sa'o'i 80 tana girki ba tare da tsayawa ba.

Labarin ta ya karaɗe ko ina a kafafen sada zumunta bayan da aka bata kambun 'Guinness World Record'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel