'Yar gayu: Jama'a Sun Gigice Da Ganin Tsafta Da Kwalliyar Gidan Wata Mata, Ta Kashe Kudade
- Wata budurwa ta burge mutane da dama bayan ta yada hotunan kayataccen gidanta a kafar sada zumunta
- Budurwar ‘yar kasar Namibia ta yada hotunan ne ta kafar sada zumunta ta Facebook inda mutane suka yaba
- Bayan daura hotunan ta yi tambaya “shin me ya kamata a rage ko a kara a gidannan?” mutane sun yi martani
Wata budurwa a kasar Namibia mai suna Johanna Shimana-Teixiera ta yada wasu kayatattun hotunan gidan da take rayuwa.
Johanna ta yada hotunan cikin gidan nata ne wanda yake kayatacce gwanin ban sha’awa ta kafar sada zumunta ta Facebook, inda ya ja hankulan ma’abota wannan shafi da dama.
Hotunan da ta yada, a cikin kankanin lokaci ya samu karbuwa sosai, yayin da fiye da mutane 500 suka tofa albarkacin bakinsu, 160 kuma suka sake yada shi.
"Soyayyar Nesa Akwai Wuya": Matashi Ya Sharbi Kuka Yayin Da Kyakkyawar Budurwarsa Baturiya Zata Koma Kasarsu
Ta yi tamabaya kamar haka:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Gida. Meye ya kamata a kara ko a rage? Kawai na nuna madafi da dakin kwana da kuma dakin yara ne.”
Matar ta burge ma’abota dandalin Facebook da sauran mutane da dama.
Ga kadan daga cikin hotunan da ta yada
Mutane sun yabi yadda tsarin gidan yake
@Kholiswa ZaMangwevu Mpayipheli Mdubane:
“Gidan ga kyau kuma a tsabtatacce. Kai.”
@Nono Sweetness:
“Ya yi kyau sosai.”
@Nayimuna Kasale:
“Ina son gidannan.
@Nta Mnisi:
“Ya yi kyau sosai.”
@Nji Milian Akwi:
“Kyakkyawan gida.”
@Apollonia Zembe Muchetu:
“Ya yi kyau ga tsafta amma kiyi kokari ki siyo kujeru masu launi masu kyau.””
@Collins Muunda:
“Ina son gidan, abin mamaki.”
@The Cooking Village Wife:
“Kai abin so ne.”
Mahaifiya ta Daure Kafar Danta a Kujera Saboda Fitina
A wani labarin, an gano wani faifan da ya yadu a kafar sada zumunta inda wata mahaifiya ta daure kafar danta a kujerar shagonta saboda barnan da yaron yake yi mata, don haka ta dauki matakin kare faruwan hakan a gaba.
Faifan bidiyon wanda wani matashi ya daura mai suna @raymist, an gano matar cikin fushi da gurnani tana nuna yadda yaron nata ya addabeta a shagon.
Ta nuna yadda ya yi kaca-kaca da shagon kuma ba ya zama haka sai ya yi mata barna, shiyasa ta dauki wannan mataki don kare faruwar hakan a gaba.
Asali: Legit.ng