Ekweremadu: Abu 5 Game Da Tsohon Mataimakin Majalisar Dattawar Najeriya Da Aka Yanke Wa Shekara 10 a Birtaniya
A ranar Alhamis 23 ga watan Yuni na shekarar da ta gabata ne kafar sada zumunta ta zamani ta dau zafi bayan da aka samu labarin kama tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice.
Legit.ng ta tattaro cewa kasashen ketare nan gida Najeriya na fakon Ekweremadu bayan ‘yan sandan Birtaniya sun kama bisa zargin da ake masa na safarar yara da siyar da wani bangare na sassan jikin wani matashi.
Bayan kamashin, an gurfanar da sanatan da matarshi Beatrice a gaban kotun majistare ta Uxbridge bayan daga bisani aka hana su beli.
Bayan dukkan wadannan abubuwa da suka dabaibaye sanatan, akwai tarun abubuwan masu ban sha’awa tattare da ma’auratan.
Ga jerin abubuwa guda 5 da ya dauki hankulan mutane a kasa:
1. Siyasar Ekweremadu
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An haifi Sanata Ike Ekweremadu a ranar 12 ga watan Mayun 1962 a kauyen Amachara Mpu da ke karamar hukumar Aninri na jihar Enugu.
Sanata Ekweremadu ya shafe shekaru fiye da 19 a majalisar tarayya bayan ya kasance shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Enugu a shekarar 1999 kafun nada shi a matsayin magatakardan gwamnatin jihar daga 2001 zuwa 2002.
Sannan ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa har na tsawon wa’adi uku (majalisa ta 6 da ta 7 da kuma ta 8) karkashin shugabancin shugaban majalisar David Mark da kuma Bukola Saraki, a jere.
An zabe shi a matsayin mataimakin kakakin Kungiyar Cigaban Kasashen Yammacin Nayiyar Afrika a watan Agusta ta shekarar 2011.
2. Takaitaccen tarihin karatun Ekweremadu
Sanata Ekweremadu ya kammala digirinsa na biyu a Jami’ar Najeriya ta Nsukka, ya kasance lauya mai gashin kansa bayan da aka kirashi a cikin kwararrun lauyoyi a shekarar 1987, sannan yana da digiri na uku a jami’ar Abuja.
3. Katobara da Ekweremadu ya gamu da su
An yi ta cece-kuce akan sanatan bayan ya bayyana ra’ayinsa da kuma fada wa ‘yan yankin kudu maso gabas da su guji zaban dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi.
Bayan wannan katobara, magoya bayan Peter Obi da sauran ‘yan Najeriya sun yi ta caccakarsa da kuma kushe wannan ra’ayi nashi, in da a wurare da dama aka rinka kawo masa hare-hare musamman harin ‘yan kabilar Ibo mazauna kasar Germany da suka yi a taronsu a Numberg.
Harin wanda ya faru a ranar 17 ga watan Agusta, an zargi ‘yan kungiyar IPOB da kai wannan harin bayan da su ka tuhumeshi akan kashe ‘yan uwansu da ake yi a kudu maso gabas.
4. Lambobin yabo da mukaman gargajiya na Ekweremadu
Sanata Ekweremadu ya samu lambobin yabo da dama da kuma sarautar gargajiya a jiharsa ta Enugu.
Ya kuma samu lambar yabo ta Dakta Kwame Nkruma ta shugabanci da sauran lambobin yabo na jami’ar Uyo da kuma na kabilarsa ta Ibo wanda Eze Nri ya nada shi, da sauran lambobin yabo da sarautar gargajiya masu tarin yawa.
5. Iyalan Sanata Ekweremadu
Sanata Ike Ekweremadu ya auri Beatrice Nwanneka mai shekaru 55, sun haifi ‘ya’ya 4 maza 2 da kuma mata 2. Daya daga cikin ‘ya’yan nasu mai suna Sonia tana fama da ciwon koda wadda ke bukatan kulawa na gaggawa da ke bukatar sauya kodar.
A kokarin su na ganin sun sama mata lafiya, an kama ma’auratan a Burtaniya a filin jirgin saman Heathrow akan hanyarsu ta zuwa Istanbul babban birnin Turkiya.
A Karshe Kotu Ta Yanke Wa Ekweremadu Hukunci Bayan Samunsa Da Laifin Yunkurin Cire Koda
Tunda farko, kun ji cewa wata kotu da ke zamanta a Landan ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu daurin shekaru tara da watanni takwas a gidan gyaran hali bisa yunkurin cire kodar wani matashi don ba wa yarsa.
Matarsa Beatrice ita kuma kotyn ta mata daurin shekaru hudu da wata shida sai kuma wani likita Obinna Obeta da ya shiga tsakani shima an masa daurin shekaru 10 tare da kwace lasisinsa na aiki.
Asali: Legit.ng