Na Sha Wahala Da Ita: Wani Ya Kashe Budurwarsa Saboda Watsi da Soyayyar Shi
- Wani matashi da aka bayyana sunansa da Keneth, yana hannun jami’an ‘yan sanda kan kisan-kai
- Wannan mutumi ya sari budurwar da suke soyayya a hannuwa da fuska, ya yi sanadiyyar ajalinta
- Kakakin ‘yan sandan Kaduna, DSP Muhammad Jalige ya nuna bakin kishi ya jawo aka yi ta’adin
Kaduna - Jami’an ‘yan sanda na reshen jihar Kaduna sun cafke wani mutumi wanda ake zargin ya kashe buduwarsa, laifin ta shi ne za ta rabu da shi.
A wasu rahotanni da muka samu daga Vanguard a ranar Juma’a, an ji Kakakin ‘yan sandan Kaduna, DSP Muhammad Jalige ya tabbatar da labarin nan.
DSP Muhammad Jalige ya ce da kimanin karfe 11:30 na ranar Juma’a, 14 ga watan Afrilu 2023, aka kira ‘yan sanda cewa wani ya kashe budurwarsa.
Hakan ya jawo mutanen gari suka nemi kashe wannan mutumi da ake zargi da laifin kisan kai.
Abin da 'yan sanda suka gani
Nan take aka tura dakarun ‘yan sanda zuwa wurin a cikin garin Kaduna, isarsu ke da wuya, sai ga wanda ake tuhuma a kwance zagaye da tulin mutane.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A wancan lokaci, wannan mutumi da aka bada sunan shi da Keneth, bai san halin da yake ciki ba, ana zargin ya aukawa Ebenezer Agada ne da makami.
Keneth ya sari Ebenezer Agada mai shekara 27 da adda a fuska da hannuwa, ko da aka garzaya da ita zuwa asibitin koyon aiki na Barau Dikko, ta cika.
Rahoton ya ce wannan mutumi ya gutserewa Marigayiyar hannu bayan ya yi mata kaca-kaca da fuska, yanzu haka ana bincike a kan gawarta a asibiti.
Jami’an tsaro sun ce Agada ta na makarantar Sakandare na Command da ke kan titin Sokoto a Kaduna. Likitoci dai sun tabbatar da cewa ta rasa ran ta.
Keneth ya kashe mata kudi
Da aka yi magana da wanda ake zargi, sai ya ce ya kashe makudan kudi a kan wannan Budurwa mai shekaru 27, amma sai ga shi ta na kokarin barinsa.
Zafin kishi ya jawo Keneth ta yi wannan aika-aika da zai cigaba da yin nadama har karshen rayuwarsa. Babu mamaki idan an gama bincike, a tafi kotu.
Barka da sallah
Watan karamar sallah ya tsaya bayan kammala azumin Ramadan, an samu rahoto cewa ana taya Musulmai musamman na Najeriya barka da shan ruwa.
Atiku Abubakar ya yi bayanin muhimmancin azumin Ramadan da halin da Najeriya take ciki a yau, shi kuma Bola Tinubu ya nemi a nunawa juna soyayya.
Asali: Legit.ng