"Yunwa Ta Kusa Kashe Ni" Ƴar Najeriya Mai Karatu a Ƙasar Waje Tayi Guzurin Kayan Abinci, Bidiyon Ya Yaɗu
- Ruwan da ya doke ka shine ruwa, wata budurwa ta koyi darasi daga wuyar da ta sha a baya
- Budurwar wacce ƴar Najeriya ce tayi guzurin kayan abinci domin tafiya da su ƙasar waje inda take karatu
- Budurwar ta bayyana dalilin da ya sanya tayi guzurin kayan abincin zuwa ƙasar waje
Wata budurwa ƴar Najeriya mai karatu a ƙasar waje tayi wani abin mamaki da ya ɗauki hankulan mutane a yanar gizo.
Budurwar dai ta kwashi kayan abinci niƙi-niƙi waɗanda zata shilla da su ƙasar wajen domin cigaba da karatun ta.
Bidiyon wanda wani mai amfani da sunan @.barine a TikTok, ya sanya ya nuna budurwar tana sanya kayan abincin cikin natsuwa a jakarta.
Budurwar ta yi guzurin doya, taliyar yara, kayan lashe-lashe da sauran kayan abinci na nan gida Najeriya da tasan zata buƙace su a inda take karatun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan ta ɗauki su doya da sauran su, ta kuma yi guzurin kayan ƙamshi, hatsi da kayan sha.
Wani abin ɗaukar hankali shine, budurwar har guzurin miya tayi a cikin wani ɗan masaki sannan ta sanya ta cikin wata babbar jaka.
Budurwar ta bayyana a cikin bidiyon cewa, yunwa ta bata wuya a wancan karon da bata tafi da guzurin ta ba.
Ta bayyana cewa wuyar da ta sha ne ya sanya ta koyi darasi inda wannan karon ta shirya tsaf kafin ta koma wajen karatunta.
Bidiyon Ya Yaɗu
Bidiyon nata ya sanya masu amfani da TikTok da dama tofa albarkacin bakin su akan sa. Ya zuwa yanzu sama da mutum miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu suka kalli bidiyon a TikTok.
Ga kaɗan daga cikin abinda suke cewa:
@F said ta rubuta:
"Ƴar'uwa ta tafi da gabadaya kasuwar a cikin jakarta."
@Yamen ya rubuta:
"Banga? Lallai kin taho da Najeriya tare dake. Na daɗe rabon da na samu doya."
@Chinedu Okeke ya rubuta:
"Ta yaya zaki iya tafiya da doya."
@Ibukun ya rubuta:
"Ki yayyanka doyar sannan ki fereta. Ki samu wani abu ki sanya ta a cikin sannan ki sanya ta firiza ta yadda ba zata lalace ba. Tana daɗewa sosai."
A wani labarin kuma, an gwangwaje wani tsoho da sha tara ta arziƙi, bayan ya fito neman aikin yi.
Wata buƙata ta dole ce ta sanya tsohon fitowa neman aikin yi duk da tsufan sa.
Asali: Legit.ng