"Ka Koma Gida Ka Kwanta" An Gwangwaje Dattijo Da Kyautar Maƙudan Kuɗaɗe

"Ka Koma Gida Ka Kwanta" An Gwangwaje Dattijo Da Kyautar Maƙudan Kuɗaɗe

  • Wani dattijo da ya kwana biyu a duniyar nan ya taki sa'a bayan an gwangwaje shi da maƙudan kuɗi
  • Dattijon ya haɗu da sa'ar ne bayan ya fito neman abinda zai yi domin ya biya wata buƙata tasa
  • Wasu ɗalibai ne dai suka tausaya wa dattijon suka ƙirƙiro hanyar da za su tallafi rayuwar sa

Wani dattijo mai shekara 80 a duniya, Mr James, ya taki sa'a bayan ya fito neman hanyar da zai biya kuɗin hayar da aka ƙara masa.

Tsohon mai shekara 80 a duniya ya fito ne yin aikin goge-goge da share-share a wata makaranta.

Dattijo
"Ka Koma Gida Ka Kwanta" An Gwangwaje Dattijo Da Kyautar Maƙudan Kuɗaɗe Asali: Instagram/Good-news movement da Bloomberg/Getty Images
Asali: UGC

An ƙara masa N184,000 akan kuɗin hayar da yake biya wanda hakan ya sanya ya kasa biyan kuɗin.

Sai dai cikin sa'a kawai sai wasu ɗalibai masu suna Marti da Banner, suka ƙirƙiri shawarar tara masa kuɗi a yanar gizo.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Mai Juna Biyu Na Addu'a Bayan An Gwangwaje Da Kyautar Sababbin Kuɗi Ya Sosa Zuciya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shafin The Good News Movement a Instagram ya rahoto cewa an tarawa Mr James maƙudan kuɗaɗen da suka kai naira miliyan arba'in da ɗaya da dubu ɗari huɗu (N41.4m)

Shafin ya rubuta a Instagram cewa:

"@goodnews_movement ya sanya Mr. James komawa ya huta a gida. A yau mun tara masa $90,000 domin yaje ya sarara abin sa. Mun gode!!!"

Abinda mutane ke cewa kan lamarin

@breeuhna ya rubuta:

"Duk da wannan abu ne mai kyau da ɗaliban suka yi, amma akwai takaici cewa ɗan shekara 80 sai ya koma neman aiki domin samun abun more rayuwa kamar gida. Yakamata wannan ƙasar ta sauya lale."

@ufgatorcouple ya rubuta:

"Abin takaici. Ba wanda yakamata ace yana aiki a waɗannan shekarun. Yakamata yayi ace suna da damar yin abinda ran su ke so."

@rosieking__ ya rubuta:

Kara karanta wannan

Gamo Da Katar: Budurwa Ta Fashe Da Kukan Daɗi Bayan An Gwangwajeta Da Miliyoyi

"Wannan abin takaici ne. Amurka ta gaza. Komawa neman tallafi domin kada ɗan shekara 80 yayi aikin goge-goge?"

Kukan Daɗi: Budurwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Samu Kyautar Maƙudan Kuɗi

A wani labarin na daban kuma wata budurwa ta ga ranar yin abin kirki, an yi mata wata kyauta ta musamman.

Bayan ganin kyautar, budurwar ta fashe da kukan daɗi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel