Matashi Ya Koka Bayan Banki Ya Lafke Shi Da Takardun Tsofaffin Kuɗi

Matashi Ya Koka Bayan Banki Ya Lafke Shi Da Takardun Tsofaffin Kuɗi

  • Wani ɗan Najeriya ya koka kan rashin kyawun kuɗin da aka ba shi da yaje banki cirar kuɗi
  • Matashin ya bayyana cewa kuɗaɗen da banki suka ba shi har wani irin wari suke yi saboda tsufa
  • Ya shawarci ƴan Najeriya kan yadda yakamata su riƙa yiwa kuɗi idan sun zo hannun su

Wani matashi ɗan Najeriya ya sanya wani bidiyo a Twitter inda ya nuna wasu takardun tsofaffin kuɗin N200 da aka bashi a banki.

Bidiyon wanda @MrMekzy_ ya nuna cewa kuɗin da aka bashi sun tsufa iya tsofewa domin duk sun gaji da duniya.

Takardun kudi
Matashi Ya Koka Bayan Banki Ya Lafke Shi Da Takardun Tsofaffin Kuɗi
Asali: Facebook

Kuɗin sun yi kama da zasu yayyage da an cika taɓa su ko akai koƙarin sanya su a cikin lalita.

Matashin yace kuɗin wari suke yi sannan dole sai ya wanke hannun shi bayan ya taɓa tsofaffin kuɗin waɗanda ke ɗauke da datti.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Zanga-Zanga Ta Sake Ɓarkewa Kan Karancin Kuɗi, An Cinnawa Bankuna Wuta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace dole ce ta sanya ya karɓi kuɗin saboda yana son ya biya wasu da suka yi masa aiki haƙƙin su.

A kalamansa:

Yanzun nan na karɓo wannan kuɗin daga banki, sun lalace ta yadda da yawa daga cikin su sun yayyage amma dai sun fi babu. Gaskiya yakamata mu riƙa da lura da yadda muke riƙe kuɗi a ƙasar nan."

Ƴan Najeriya da suka yi arba da bidiyon sun bayyana cewa da wuya mutanen da yake so ya biya haƙƙin su da kuɗin su karɓa, domin sun yi tsofaffi da yawa.

Wannan na zuwa a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke cigaba da kokowar samun kuɗin da zasu riƙa gudanar da harkokin su na yau da kullum.

Meyasa Zata Yi Min Wannan Ɗanyen Aiki? Magidanci Ya Koka Kan Halin Matarsa

A wani labarin na daban kuma, wani magidanci ya koka biyo bayan gano wani ɗanyen aiki da matarsa tayi masa. Ya koka matuka kan wannan halin na matar tasa.

Magidancin ya bayyana cewa bai sani ba ashe matarsa na da tarin kuɗi a ɓoye amma ta bar shi yana ta shan wuya abin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel