Kwankwaso Ya yi Jimamin Mutuwar Farfesan da ke Taimakawa Takararsa a NNPP
- Jami’ar Jihar Kaduna ta KASU, ta rasa Farfesa Aminu Yusuf Usman a karshen makon da ya gabata
- Rabiu Musa Kwankwaso Masanin tattalin arzikin yana cikin ‘yan kwamitin yakin neman zabensa
- ‘Dan takaran shugabancin kasar ya aika sakon ta’aziyya ga iyali da ‘yanuwan Aminu Yusuf Usman
Kaduna - A karshen makon nan ne jami’ar jihar Kaduna wanda aka fi sani da KASU, ta rasa kwararren malamin ta, Farfesa Aminu Yusuf Usman.
Rabiu Musa Kwankwaso mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, ya na cikin wadanda mutuwar Farfesa Aminu Yusuf Usman ta taba.
A wata sanarwa da ya fitar a yammacin Lahadi, 22 ga watan Junairu 2023, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi jimamin mutuwar shehin malamin.
Da yake magana a dandalin Twitter, Sanata Kwankwaso ya shaidawa cewa malamin jami’ar yana cikin ‘yan kwamitin yakin neman takarar da yake yi.
Ta'aziyyar Sanata Rabiu Kwankwaso a Twitter
‘Dan siyasar ya yi wa masanin tattalin arzikin addu’a, tare da aika ta’aziyya ga ‘yanuwa da abokansa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Innalillahi wa Inna Ilaihi Rajiun.
Ina mai takaicin rashin Farfesa Aminu Usman na jami’ar KASU kuma daya daga cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasarmu.
Allah ya yafe masa kura-kurensa. Ina mika ta’aziyyata ga damgi, abokai da abokan aikinsa.
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Daily Trust ta ce an birne Farfesa Usman ranar Lahadi a garin Zariya bayan an yi masa sallar jana’iza a masallacin Kofar Gayan da ke cikin garin.
Farfesan masani ne a kan tattalin arziki, shi ne shugaban kamfanin Al-amin Global Consult Ltd.
An yi rashin masanin tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta fahimci Marigayin ya yi digirorin B. SC, M. Sc da PhD ne a ABU Zaria, Jami’ar Jos da NDA a shekarun 1988, 1993 da kuma 2012.
A lokacin rayuwarsa, ya yi rubuce-rubuce da bincike da-dama a kan sha’anin kudi, tashin kudin kasar waje da tsare-tsare da manufofin bankin CBN.
G5 da siyasar 2023
An samu labari wani jagoran PDP a karamar hukumar Ikwerre da Rotimi Amaechi ya fito, ya bayyana ‘dan takaransu na shugaban kasa a zaben 2023.
Hon. Samuel Nwanosike ya tabbatar da cewa ba za su goyi bayan Atiku Abubakar ba, alamu na nuna Gwamna Nyesom Wike zai tallata APC a jihar Ribas.
Asali: Legit.ng