Masu Kudi 3 Rak, Sun Zarce ‘Yan Najeriya Miliyan 83 a Dunkule Wajen Yawan Dukiya

Masu Kudi 3 Rak, Sun Zarce ‘Yan Najeriya Miliyan 83 a Dunkule Wajen Yawan Dukiya

  • Manyan Attajiran Duniya su na ta kara arziki yayin da marasa hali suke kara rungumar talauci
  • Rahoton ‘Davos 2023 Inequality Report’ ya nuna yadda masu kudi suke kara yi wa talaka fintinkau
  • Kudin da manyan masu kudin Najeriya suka tara, ya zarce abin da mutum miliyan 80 suke da shi

Abuja - Idan za a tara dukiyar mutane miliyan 83 a Najeriya, Attajirai uku kurum da ake ji da su, sun sha gaban wadannan tulin jama’a a yawan kudi.

Daily Trust ta ce wani rahoto mai suna ‘Davos 2023 Inequality Report’ da aka fitar ranar Litinin dinnan a garin Abuja, shi ya tabbatar da wannan bayani.

Shugaban Oxfam a Najeriya, Dr. Vincent Ahonsi ya gabatar da rahoton nan a daidai lokacin da ake shirin yin babban taron Duniya a Davos Switzerland.

Kara karanta wannan

Sharri aka min: Dan sandan da bindige lauya mai juna biyu ya musanta zargin kisa

Mataimakiyar darektan sashen kula da kasafi ta Oxfam, Regina Afiemo ta wakilci Dr. Vincent Ahonsi wajen gabatar da rahoton a babban birnin Abuja.

Akwai bukatar a karawa Attajirai haraji

Sauran wadanda ke wajen su ne shugaban CODE, Hamza Lawal da Kenneth Akpan sai Henry Ushie mai jagorantar makamanciyar wannan kungiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda suka gabatar da rahoton sun hadu a kan cewa dole ne a lafta haraji a kan attajiran Duniya domin rage irin rashin adalcin da ake samu a yau.

Masu Kudi
Wasu daga cikin masu kudin Najeriya Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

A shekarun bayan nan, rahoton ya ce rabin dukiyar Duniya ta na hannun manyan attajiran da ake da su, alhali dinbin mutane su na rayuwa a talauci.

Binciken da aka yi ya nuna arzikin masu kudin Duniya yana karuwa da $2.7bn a kowace rana.

Da a ce wadannan masu kudi za su biya harajin 5%, za a iya tashi da $1.7trn a duk shekara, kudin da za su yi wa mutane biliyan biyu maganin talauci.

Kara karanta wannan

2023: Bidiyon Yadda Aka Ceci Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Tulin Jama'a Ya Fito

Kudin Najeriya su na hannun tsiraru

Jaridar Vanguard ta ce attajirai 83 da ke kasar nan suka tashi da fiye da 60% na duka Dala tiriliyan 42 da aka samu a Najeriya daga shekarar 2020 zuwa yau.

A gida Najeriya akwai mutane 6,355 da suka mallaki fiye da Dala miliyan 5, abin da hakan yake nufi shi ne arzikinsu ya fi na mutum miliyan 107 a dunkule.

Za a kama Gwamnan CBN?

An ji labari cewa wasu fitattun Lauyoyi da ake ji da su sun aika wasika zuwa ga Ministan shari’a, Abubakar Malami a kan batun cafke Gwamnan CBN.

Lauyoyin da suka aikawa AGF wasika su ne: Adetokunbo Kayode, Oba Maduabuchi, Emeka Ozoani, M.M Nurudeen, Abdul Mohammed, da Emeka Obegolu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel