Na Kashewa Marigayiya Ummita N60m a Kan Mota, IPhone, Gwal Inji Mutumin China

Na Kashewa Marigayiya Ummita N60m a Kan Mota, IPhone, Gwal Inji Mutumin China

  • An koma kotu da ‘Dan Chinar nan, ya fadi irin makudan dukiyar da ya batar a kan Ummulkusum Buhari
  • Frank Geng Quanrong ya jero kudin da ya kashewa Ummita a lokacin da suke soyayya lokacin tana da rai
  • Quanrong ya ce ya sayawa Marigayiyar gwala-gwalai, gida, mota, wayoyi da sun ci masa kimanin N60m

Kano - Mutumin kasar Sin dinnan, Frank Geng Quanrong wanda ake tuhuma da laifin hallaka buduwarsa ya sake bayyana gaban kotu domin shari’a.

Wani rahoto na Aminiya ya nuna Mista Frank Geng Quanrong ya yi ikirarin sai da ya kashe Naira miliyan 60 a kan Ummulkusum Buhari watau Ummita.

Da aka koma zama a babban kotun jihar Kano, Quanrong ya yi wa Alkali bayanin makudan kudin da ya batar a kan masoyiyarsa da ake zargin ya kashe.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Ce Ya Cika Alkawuran da Ya Dauka, Tinubu Ya Ce ba Haka Abin Yake ba

A cewarsa, ya kashe miliyoyin kudin ne a yayin da suke soyayya na tsawon shekaru biyu.

An je otel, na saya mota da gida - Frank Geng Quanrong

Basinen ya ce abin ba a kudi kurum ya tsaya ba, ya rika kai Marigayiya Ummita zuwa gidajen cin abinci da kuma manyan otel irinsu Bristol da Central.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Baya ga otel da aka rika zagayawa, Mista Frank Geng Quanrong ya ce sai da ya kashe N4m wajen sayawa Ummulkusum Buhari gida da kuma motar N10m.

Akwai gwala-gwalai na Naira miliyan biyar da wayoyin zamani kirar iPhone har biyu na sama da Naira miliyan daya, sannan ya dauki nauyin gidansu.

Ummita
Marigayiya Ummita Buhari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Quanrong yake cewa akwai lokacin da ya biya Naira miliyan 1 saboda a kafa na’urar sola a gidan su Marigayiya Ummita, yana sa ran za su zama surukansa.

Kara karanta wannan

An Tono Babban Abinda APC Ta Rasa a Arewa Wanda Zai Ja Wa Tinubu Shan Kaye a Zaben 2023

Bugu da kari, jaridar ta rahoto Basinen yana cewa ya ba Marigayiyar kyautar N18m a matsayin jari domin ta soma kasuwancin saida takalma da jakunkuna.

Shi kan shi shagon ya ci N200, 000 ban da turamen atamfofi da kuma leshi na akalla N1m.

Idan maganar wanda ake tuhuma gaskiya ne, mutumin Sin din ya taba ba Ummita Naira miliyan shida da sunan za ta karbo satifiket daga jami’ar Sokoto.

An rahoto shi yana cewa da aka fara shirin aure, ya kashe N1.5m a wajen lesoshi da atamfofi da mayafai masu tsada, sannan ya bada N700, 000 na likin biki.

Abin bai tsaya a nan ba, ya ce akwai kudin da ya batar da nufin ankon amarya, sannan ya kashe N700, 000 wajen neman aure wajen mahaifinta a Sokoto.

Wata rana Ummita ta nemi kudi a wurin Frank Geng Quanrong, sai ya fada mata bai da hali, yake cewa tun daga nan sai ta daina daukar wayarsa idan ya kira ta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Yi Sabuwar Nadi Mai Muhimmanci Gabanin Babban Zaben 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng