Boka Ya Yi Mummunan Karshe, Ya Mutu a Wajen Lalata da Uwargidar Wani Fasto

Boka Ya Yi Mummunan Karshe, Ya Mutu a Wajen Lalata da Uwargidar Wani Fasto

  • Fadayomi Kehinde ya rasu bayan ya gama lalata da matar wani malamin addini da aka boye sunanta
  • Abin takaicin ya faru ne a Ikere Ekiti a jihar Ekiti wanda hakan ya fusata wasu mabiyan wannan boka
  • ‘Yan garin sun ce matar faston tana dauke da tsafin Magun wanda mazan Yarbawa suka saba yi

Ekiti - Wani mutumi mai matsakaicin shekaru da ake tunanin cewa boko ne, ya rasu a lokacin da yake fasikanci da mai dakin wani malamin addini.

Leadership ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 5 ga watan Junairu 2023 cewa wannan abin ya faru a yankin Ikere Ekiti da ke jihar Ekiti a makon jiya.

Fadayomi Kehinde wanda boka ne da aka fi sani da Ejiogbe ya mutu ne yayin da yake cikin wani otel a garin na Ikere Ekiti tare da matar fasto a garin.

Kara karanta wannan

Wani Magidanci, Nuhu Usman, Ya Bindige Matarsa Har Lahira A Bauchi

Ana gama lalatar sai Fadayomi Kehinde ya fara birgima, hakan ya jawo uwargidar wannan malamin addini na kirista ta nemi taimakon jama’a.

An ruga da Boka zuwa asibiti

Rahoton ya ce nan take wasu daga cikin ma’aikatan otel din suka yi gaggawar shekawa da shi zuwa wani asibiti, a nan aka tabbatar ya cika.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiya ta ce abin da ya kashe malamin tsibbun shi ne “Magun” – wanda wani tsafi ne da ake yi wa matan auren da ke hulda da maza a kasar Yarbawa.

'Yan sanda
'Yan sanda a bakin aiki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Aikin Magun ne

Yarbawa sun canfa cewa idan aka yi tsafin, mutum zai hallaka idan ya taba matar wani.

Saboda haushin abin da ya faru, abokan aiki da na-kusa da faston sun je cocin mijin abokiyar lalatar marigayin, suka yi watsa-watsa da majami’arsu.

Aminiya ta tabbatar da cewa wannan mata kuwa da ba a fito da sunanta ba, ta na hannun ‘yan sanda domin a gudanar da bincike game da lamarin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mazauna sun rikice, an sace musu mai gidan saukar baki

'Yan sanda su na yin bincike

Mai magana da yawun bakin jami’an ‘yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu ya tabbatar da aukuwar lamarin, bayan samun labari, sun je otel din.

Abutu yake cewa an dauki wannan mutumi zuwa asibiti, inda likitoci suka shaida ya rasu. Ita matar tana fuskantar barazanar fushin mabiyan bokan.

Soja ya kashe rai a Abuja

Rahoto ya zo cewa wasu Sojoji sun yi yunkurin tare mutanen da suka biyo titi cikin duhun dare a Asokoro da ke garin Abuja, a karshe dai aka rasa rai.

A sanadiyyar haka ne wani soja ‘dan bindiga-dadi ya dana kunamarsa, nan-take ya aika wani fasinja zuwa barzahu, nan aka bar gawarsa a kan hanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng