Dalibar da ta fi Kowa Tsufa a Duniya Ta Mutu a Makarantar Firamare a Shekara 99
- Misis Priscilla Sitieni ta kwanta dama kamar yadda ‘yanuwanta suka tabbatarwa manema labarai
- Kafin rasuwarta, Priscilla Sitieni ce dalibar da ta fi kowa tsufa a makarantar firamare a Duniya
- Marigayiyar ta cika tana shekara 99, har zuwa lokacin da ajali ya zo mata, ba ta gama firamare ba
Kenya - Priscilla Sitieni wanda ita ce ake tunanin daliba mafi tsufa a makarantar firamare a Duniya, ta mutu tana ‘yar shekara 99 da haihuwa.
Wata jaridar kasar Kenya, The Standard newspaper ta fitar da rahoto cewa Gogo Priscilla kamar yadda jama'a suka fi saninta, ta bar Duniya.
Priscilla Sitieni ta mutu ne a ranar Larabar da ta gabata biyo bayan fama da ta yi da ciwon kirji, ta mutu ne a gidanta a kasar gabashin Afrikan.
Wata majiya daga dangin wannan tsohuwa sun bayyanawa manema labarai cewa har kwanaki ukun kafin ranar da za ta rasu, tana shiga aji.
Priscilla Sitieni ta zama abin alfahari
‘Yanuwan marigayiyar sun shaida cewa Sitieni ta jawowa dangin na su abin alfahari a Duniya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton da AFP ta fitar ya bayyana cewa Marigayiya Priscilla Sitieni ta shiga makarantar firamare a kauyensu tana shekara 94 da haihuwa.
A dalilin wannan, hukumar nan ta UNESCO ta yaba mata, tace dattijuwar ta zama abin yin koyi.
Da majalisar dinkin Duniya tayi hira da ita, dattijuwar tace ta koma aji ne domin ta karfafawa matan Kenya su koma makaranta bayan tara yara.
Sitieni ta mutu da buri
BBC tace mutuwar ta zo ne a lokacin da Sitienei mai neman cika shekara 100 da sauran ‘yan ajinta suke shiryawa jarrabawar zangon da ake ciki.
Ko da ba ta samu takardar shaidar kammala firamare ba, Marigayiyar ta fara cin ma burinta na ganin ta iya rubutu da karatu a shekarunta na tsufa.
Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai Omo Ovie-Agege Yace Shine Ya Dakatar da Kudirin Tsige Shugaba Buhari
Wannan mata shiga makarantar firamaren Leaders Vision Preparatory da ke kauyen Ndalat bayan tayi tsawon shekaru 65 tana aikin jinya a asibiti.
Mueez Akande ya rasu
An samu labari wani na kut-da-kut, tsohon Kwamishina kuma ‘Danuwan Uwargidar Bola Tinubu, Mueez Akande ya rasu yana shekara 72 da haihuwa.
Dr. Mueez Akande yana cikin wadanda aka matsawa lamba, ana zargin yana da hannu wajen safarar kwayoyi tsakanin 1988 da 1992 zuwa Najeriya.
Asali: Legit.ng