Daliba Yar Firmare Mafi Tsufa A Duniya Ta Mutu A Kenya Tana Da Shekaru 99

Daliba Yar Firmare Mafi Tsufa A Duniya Ta Mutu A Kenya Tana Da Shekaru 99

  • Priscilla Sitieni, dalibar firmare mafi tsufa a duniya wacce ta samu yabo daga UNESCO ta kwanta dama tana da shekaru 99 a duniya
  • Sammy Chepsiror, jikon Sitieni ya tabbatar da rasuwarta, yana mai cewa ta yi fama da ciwon kirji na kwana uku
  • Sitieni ta ce ta koma makaranta tana da shekaru 94 ne don karfafawa iyaye mata a duniya gwiwa su rika komawa makaranta bayan sun haihu

Kenya - Dalibar makarantar frimare mafi tsufa a duniya, Priscilla Sitieni, wacce kudirinta na neman ilimi a yayin da ta haura shekaru 90 ya janyo yin fim a Faransa kuma ta samu yabo daga UNESCO, ta rasu tana da shekaru 99, kamar yadda kafofin watsa labarai suka ruwaito.

Guardian ta rahoto cewa Jikanta, Sammy Chepsiror, ya shaidawa jaridar The Standard cewa Gogo Priscilla (Kaka Priscilla) kamar yadda aka saba kiranta, ta rasu a gida a ranar Laraba bayan kamuwa da ciwon kirji.

Kara karanta wannan

Rikici: An tasa keyar fasto zuwa magarkama bayan cinye kudin wata malamar makaranta

Gogo Priscilla
Daliba Yar Firmare Mafi Tsufa A Duniya Ta Mutu A Kenya Tana Da Shekaru 99. Hoto: @TheGuardianNG
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kara da cewa:

"Lafiyar Gogo kalau kuma tana zuwa makaranta har zuwa kwanaki uku kafin rasuwarta lokacin da ta kamu da ciwon kirji, wanda ya hana ta zuwa makaranta.
"Muna godiya bisa shekaru 100 na rayuwarta. Ta saka mu alfahari da ita."

Yadda ta shiga makaranta

Shekarunta 94 a lokacin da ta roki shugaban makarantar frimare a kauyenta ya amince ta fara zuwa makarantar, a cewar UNESCO, wacce ta jinjinta mata a 'matsayin abin koyi ga mutanen garinta da ma duniya.'

A hirar da UN ta yi da ita a bara, ta ce burinta shine karfafawa iyaye mata a Kenya gwiwa su koma makaranta bayan sun haifi yara, a maimakon dena zuwa makaranta saboda gudun tsangwama daga al'umma, rahoton The Punch.

Ta ce:

"Ina son nuna misali ne ba kawai gare su ba amma ga dukkan mata a fadin duniya da ba su zuwa makaranta.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Magidanci a Yobe da Garkame Matarsa Tsawon Shekara 1, Baya Bata Abinci Sai Koko

"Idan ba ilimi, ba bu banbanci tsakanin ka da kaza.
"Ilimi ne abin da zai taimake ka a gaba. Ilimi zai tsaya a kanka har abada kuma ba za ka rasa shi idan har ka samu."

An shirya fim a Farasan mai suna 'Gogo' don adana jajircewarta, hakan ya yi sanadin ta shiga jirgin sama karon farko a rayuwarta ta ziyarci Faransa ta gana da matar shugaban kasa, Brigitte Macron.

Daya cikin marubuta fim din ya yi ta'aziyar rasuwarta a ranar Alhamis a Tuwita yana mai cewa:

"Sakon ta game da ilimin mata bai zai gushe ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel