‘Dan China Ya Shaidawa ‘Yan Sanda Ainihin Abin da ya sa ya Aika Ummita Barzahu

‘Dan China Ya Shaidawa ‘Yan Sanda Ainihin Abin da ya sa ya Aika Ummita Barzahu

  • ‘Yan sanda sun ce Geng Quangrong ya yi masu bayanin abin da ya jawo ya kashe Ummukulsum Sani Buhari
  • Jami’an ‘yan sanda sun yi wa kotu wannan bayani da aka koma gaban Alkali domin cigaba da sauraron kara
  • Sufeta Chindo Shuwa yace wanda ake karar yana ikirarin Marigayiyar ce ta mare shi, sai ya caka mata wuka

Kano - Jami’an ‘yan sanda sun yi wa kotu bayanin dalilin Geng Quangrong na hallaka Ummukulsum Sani Buhari da ake tuhumarsa da kashewa.

Aminiya ta rahoto cewa jami’an ‘yan sanda sun shaidawa kotun da ke sauraron karar Geng Quangrong, ya cakawa Ummita wuka ne saboda ta mare shi.

A cewar wannan mutum ‘dan kasar Sin, Marigayiya Ummukulsum Sani Buhari ta sharara masa mari ne bayan an karbe wani karenta daga hannunsa.

Kara karanta wannan

Jami’an Tsaro Sun Damke Mai Garkuwa da Mutane Yana Tsaka da Siyan Abinci a Kwara

Sufeta Chindo Shuwa ya fadawa kotu shi wanda ake tuhuma ya yi masa wannan bayani a lokacin da aka yi masa wasu tambayoyi a ofishin ‘yan sanda.

Kanwar Ummita ta karbe kare

Shuwa yace Quangrong ya fada masu kanwar marigayiyar ce ta bude kofa, ta karbe karen da aka ba shi, ba tare da an bude masa gidan domin ya shigo ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shi kuma da ya ga abin haka ne, sai ya yi ta buga masu kofa har mahaifiyar Ummita ta bude gidan, daga shigarsa sai ya dauki karensa, ya kama hanyar fita.

'Dan China
Geng Quangrong da Ummukulsum Sani Buhari Hoto: news.yahoo.com
Asali: UGC

Sai ga saukar mari

Idan abin da Quangrong ya fada ta tabbata, daga nan sai Ummita wanda ta riga mu gidan gaskiya ta dumfaro shi domin ta karbe karenta, ta yaba masa mari.

Baya ga mari, yace Ummukulsum Buhari tayi masa barazanar kira masa ‘yan sanda, shi kuma daga nan ya ciro wuka daga aljihunsa, ya caka mata sau biyu.

Kara karanta wannan

Rikici: An tasa keyar fasto zuwa magarkama bayan cinye kudin wata malamar makaranta

Bangaren gwamnati da suka shigar da kara sun gabatarwa kotu wukar a matsayin hujja.

Jaridar tace Lauyan wannan mutumi da ake kara, Muhammad Danazumi ya yi ikirarin an gartsa masa cizo a hannunsa da yatsa, yace aikin marigayiyar ne.

Mai shari’a Sanusi Ado Maaji wanda karar take gabansa, ya dage zaman kotun zuwa yau Juma’a.

'Dan China ya yaudare Ummita

Kwanaki aka labari wata kawar Ummukulsum Buhari wanda aka fi sani da Ummita, tayi karin haske a kan alakar mai rasuwar da masoyinta a wancan lokaci.

Wannan Baiwar Allah tace akwai alamun tambaya game da musuluntar da Geng Quanrong yake ikirari, kuma tun tuni Ummita tayi ta kokarin ta rabu da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng