Gwamnatin Amurka Ta Bayyana Hukuncin da Take So Ayi Wa Hushpuppi a Kurkuku
- Lauyoyin da suka tsayawa Gwamnatin kasar Amurka a shari’ar Ramon Abbas suna so a daure shi
- Ana tuhumar Ramon Abbas watau Hushpuppi da damfarar mutane, kuma ya amsa aikata wannan laifi
- Gwamnatin Amurka tana so a rufe Hushpuppi a kurkuku na shekara 11 maimakon ayi masa lamuni
United States - Gwamnatin kasar Amurka ta roki kotun yankin tsakiyar Kalifoniya a Amurka ta yankewa Ramon Abbas ‘Hushpuppi’ hukuncin dauri.
Premium Times ta rahoto Gwamnatin Amurka tana cewa Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi ya cancanci daurin watanni 135 a kurkuku.
Lauyoyin Amurka sun bayyana cewa ya kamata Hushpuppi ya yi shekaru 11 da watanni uku a tsare saboda laifin da ake zarginsa da aikatawa.
Lauyoyin da suke kare Ramon Abbas suna nema masa afuwa a gaban Alkali, amma gwamnatin kasar Amurka ta nuna ba ta yarda wannan maganar ba.
Kamar yadda rahoto ya bayyana, lauyoyin sun nuna duk da ya bada hadin-kai, Hushpuppi ya yi kaurin suna a rayuwarsa wajen damfarar mutane.
“Wanda ake tuhuma mutum ne mai buri, amma burinsa ya karkata ne wajen aikata laifuffuka da romon da aka samu.”
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Masu kare Hushpuppi sun bada misali da wasu mutum hudu ‘yan Najeriya da aka yi wa afuwa a shari’ar da aka yi da su a kan harkar damfarar jama'a.
Lauyoyin kasar Amurka sun maida martani da cewa akwai bambanci tsakanin shari’ar da aka yi da wadannan mutane da Hushpuppi mai shekara 39.
Rahoton yace lauyoyin da suka shigar da kara sun fadawa Alkalin kotun na kalifoniya cewa sauran misalan da aka bada ba su da alaka da na su.
“A wadannan shari’o’i ba a samu makudan kudi masu yawa ba, aka tafka damfarar makudan miliyoyin daloli.”
- Stephanie Christensen
Stephanie Christensen mai jagorantar lauyoyin gwamnati yayi watsi da rokon masu kare Abbas, yace a yanke masa hukuncin watanni 135 a gidan maza.
Ban saci kudi ba - Chimaroke Nnamani
Kun samu labari ana yawo da jita-jita cewa FBI ta bankado Sanata Chimaroke Nnamani ya saye gidaje a Amurka da yake kan kujerar Gwamna
‘Dan siyasar da ya matsawa magoya bayan Peter Obi lamba, ya wanke kan shi a wani jawabi, yace abokan adawar siyasa ne kurum suke yi masa sharri.
Asali: Legit.ng