Yadda ‘Dan China Ya Yaudari Ummita Kan Shiga Musulunci inji Babbar Kawar Marigayiya

Yadda ‘Dan China Ya Yaudari Ummita Kan Shiga Musulunci inji Babbar Kawar Marigayiya

  • Rabia N. Garba tana cikin manyan aminan Marigayiya Ummukulsum Sani Buhari a lokacin da take raye
  • Wannan Baiwar Allah tace akwai alamun tambaya game da musuluntar da Geng Quanrong yake ikirari
  • Kawar Marigayiyar tace tun tuni Ummita tayi ta kokarin ta rabu da wanda ya yi sanadin mutuwarta

Kano - Wata kawar Ummukulsum Sani Buhari wanda aka fi sani da Ummita, tayi karin haske a kan alakar mai rasuwar da masoyinta, Geng Quanrong.

Rabia N. Garba wanda ta bayyana kan ta a matsayin aminiyar Marigayiyar, ta shaidawa Daily Trust abin da ya wakana tsakanin kawarta da Quanrong.

Kamar yadda Rabia Garba ta fada, sun san wannan mutumin kasar Sin ne da suna Frank, daga baya yayi ikirarin ya koma Faisal bayan yace ya musulunta.

Geng Quanrong yace ya karbi musulunci ne saboda kaunar da yake yi wa Marigayiya Ummita.

Kara karanta wannan

An Jefar da Karar da Abduljabbar Kabara Ya Kai Gwamnati, An Ci Shi Tarar N100, 000

“Kamar dai yadda na dan san shi, shi mutum ne mai yawan fushi, har a kan abin da bai kai ya kawo ba.
Ko dadewa aka yi ba a shi amsa a lokacin da ake hira, sai wannan ya fusata shi.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Rabia N. Garba

Ummita
Marigayiya Ummukulsum Sani Buhari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Auren 'Frank' zai yi wahala

“Zan iya cewa alakarsu kamar abokantaka ce domin marigayiyar ta san cewa ba za ta taba iya aurensa ba.
Tayi kokarin hana shi soyayya da ita, amma daga baya ta fara son shi saboda ya yi ikirarin karbar musulunci.
Ya yi da’awar musulunta, wannan abin ya jawo ta fara soyayya da shi. Har yace ya fara koyon yin sallah."

- Rabia N. Garba

Jaridar ta rahoto wannan Baiwar Allah tana cewa akwai abin tambaya a kan karbar addinin musuluncin da Geng Quanrong yake ikirarin cewa ya yi.

Kara karanta wannan

Aika-Aikar Dan China: Gwamnatina Za Ta Dauki Mataki Kan Makashin Ummita, Inji Ganduje

A cewar Rabi N. Garba, sun gano Frank (kamar yadda suka san shi) ya cigaba da amfani da sunansa, duk da ya fada masu ya canza suna zuwa Faisal.

Baya ga haka boye gaskiyar sunansa, wannan mutum bai taba fada masu cikakken sunansa ba, kuma ya fadu masu shi ‘dan kasuwa ne a kantin Kwari.

Har lokacin da Ummita take gidan aure, Quanrong ya taba fadawa aminiyar cewa yana son ta, ta nuna masa ba zai yiwu ayi soyayya da matar aure ba.

Yadda muka yi da ita - Daurawa

A yau kun ji labari cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana tattaunawar da suka yi da Ummakulsum Buhari kafin a kashe ta a gidan iyayenta.

Shehin malamin yace ya ba Marigayiyar shawarwari a game da shirinta na auren Mista Gheng Quanrong bayan ta fada masa cewa ya karbi musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng