Yara da kudi: Matasa da suka fi Kowa Kudi da Yadda Suka Zama Biliniyoyi a Najeriya

Yara da kudi: Matasa da suka fi Kowa Kudi da Yadda Suka Zama Biliniyoyi a Najeriya

Hausawa su na cewa yaro da kudi, abokin tafiyar manya. Wannan rahoto na Legit.ng ya tattaro jerin matasan da suke da makudan kudi ne a Najeriya.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kamar yadda za a gani, wadannan mutane masu matsakaitan shekarun sun yi arziki ne ta sanadiyyar watsa labarai, kimiyya da fasaha da harkar gidaje.

Watakila a cikin wadannan masu tasowa a samu wanda zai zama irin su Aliko Dangote nan gaba.

1. Igho Sanomi

Rahoton Newswirengr ya nuna Igho Snomi yana cikin attajiran matasa a Najeriya. Shugaban kamfanin na Cosmos oil AG da Taleveras ya ba $1bn baya.

Igho Sanomi ya yi kudi ne da harkar sadarwa, shigo da kaya ta jiragen ruwa da jiragen sama, sannan ya sa kudinsa a Taleveras wajen mai da kuma gas.

2. Ladi Delano

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Amaechi: Daliget Da Suka Sayar Da Kuri'unsu Yayin Zaben Fidda Gwani Na APC Suna Nadama

Idan ana maganar matasa masu kudi a kugunsu, akwai Ladi Delano wanda yana cikin wadanda suka kafa kamfanin na Moove wanda ake ji da shi a Afrika.

Delano ne ya kafa Solid XS wanda aka saya a 2008 a $15m. Daga nan suka cire $1bn, suka kafa kamfanin Bakrie Delano Africa, su na harkar sadarwa da fetur.

3. Obi Cubana

An fi sanin Obinna Iyiegbu da Obi Cubana a Najeriya, shi ne shugaban kamfanin Cubana Groups. A cikin taurari, ana tunanin babu mai kudinsa, Dala miliyan 500.

Obi Cubana
Obi Cubana yana fara'a Hoto: theparadise.ng
Asali: UGC

Obi Cubana ya yi kudi ne wajen saye da saida manyan kadarori, kwanan nan ya saye Odogwu Bitters. 'Dan kasuwan mai shekara 47 ya shiga cikin wannan jerin.

4. Jowizaza

Joseph Eze Okafor wanda aka fi sani da Jowizaza, matashin mai kudi ne a kudancin Najeriya. Legit.ng Hausa ta ce Jowizaza ya ci gadon dukiyar mahaifinsa ne.

Ga wadanda ba su da labari, Joseph Eze Okafor shine shugaban kamfanin Jezco Oil Nigeria Ltd a yau. Dukiyar matashin sun fito ne wajen sha’anin gas da man fetur.

Kara karanta wannan

2023: Sanusi II ya yi Jawabi a Game da Zabe, ya Bayyana cikas 1 da ake Fuskanta

5. Seyi Tinubu

Seyi Tinubu ‘da ne ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda kowa ya san shi a siyasar Najeriya. Ana tunanin matashin ya ba Dala miliyan 1.5 (N600m) baya a yau.

Rahotanni sun nuna Seyi Tinubu ne ya mallaki kamfanin Loatsad Promo media Ltd, wannan kamfani ya shahara, kuma ya yi kudi ne wajen yin tallace-tallace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng