Angon Instagram: Yadda budurwa ta cire kunya tayi abin da ya dace, ta yi wuf da matashi

Angon Instagram: Yadda budurwa ta cire kunya tayi abin da ya dace, ta yi wuf da matashi

  • Wani mutum mai suna Idris Gombawa ya ba da mamaki a kafar yanar gizo dangane da yadda ya hadu da matarsa abin kaunarsa
  • Idris ya tuno yadda ya hadu da wata kyakkyawar budurwa a wani kantin magani amma ya kasa yin karfin halin yi mata magana
  • Kyakkyawar budurwar ta aika masa sako a dandalin sada zumunta na Instagram don tabbatar da ko shi ne wanda ta gani, daga nan abubuwa suka canza

Wani dan Najeriya ya tuna da irin rawar da ya taka a shekarar 2021 yayin da ya dauki shafin sada zumunta a matsayin hanyar neman soyayya ta gaskiya.

Matashin da yayi wuff da masoyiyarsa
Angon Instagram: Yadda budurwa ta cire kunya tayi abin da ya dace, ta yi wuf da matashi | Hoto: GettyImages
Asali: UGC

Budurwar ce ta fara nuna sha'awa

Idris Gombawa, a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya tuno yadda ya hadu da wata kyakkyawar mace a wani kantin magani, amma ya rasa karfin gwiwar yi mata magana.

Kara karanta wannan

Wani mutum ya dawo daga kasar waje, ya tarar wani yana gina katafaren gida a filinsa, mutane sun magantu

A cewar mutumin, budurwar ta tuntube shi a shafin Instagram don jin ko shi ne mutumin da ta gani a kantin maganin.

Wannan matakin da budurwar ta dauka ya kulla abokantaka tsakaninsu wanda ya kai ga kullawar soyayya da alaka mai karfi cikin kasa da wata guda bayan haduwarsu ta Instagram.

Sun shiga daga ciki bayan watanni 8 kacal

Sun cike kyakkyawan labarin soyayyarsu da aure watanni 8 bayan haduwarsu.

Angon ya rubuta a shafinsa cewa:

"Babban abin da na samu a #2021 shine lokacin da wata kyakkyawar mace da (na gani a Hmedix kuma na kasa yin karfin hali yi mata magana) ta aiko min da sako ta IG tana tambayar ko ni ne ta gani.. Sauran batun ya zama harihi!
"Watar da ta biyo muka kulla alaka muka yi aure bayan watanni 8. Alhamdulillah."

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Yadda raken N50 ya jawo rikicin da ya kai ga zub da jini da garkame kasuwa a jihar Kwara

Martanin 'yan soshiyal midiya

Kafar labarai ta Tuko.co.ke ta tattaro martanin mutane a kafar yanar gizo.

@taramasalata001 said:

"@IdrisGombawa Kai... Ka ji labarin soyayya.
"Da a Indiya ne da yanzu sun kaddamar da fim a kan wannan labarin."
"Masha Allah... Allah ya albarkaci gidanku."

@Sir_Ruffy ya rubuta:

"@IdrisGombawa Alhamdulillah. Ina tayaka murna. Na tuna sadda muka yi magana akan wannan kuma ganin yadda komai yayi kyau. Allah Ya kara arziki."

@mamimahh ta ce:

"@IdrisGombawa Ahh Masha Allah.
"Allah ya sanyawa rayuwar aurenku albarka ya kawo zuria dayyiba.

@SadeeqAhmad99 ya ce:

"@IdrisGombawa Ta so ka ce sannu ne."
"Na hadu da wata yau gwanin sha'awa na yi karfin hali na ce sannu."

A wani labarin, ASP Abdulmuhyi Bagel Garba ya yi babban rashi a Duniya, yayin da wanda yake shirin ya aura a watan Fubrairun shekarar nan ta 2022 ta rasu.

Abdulmuhyi Bagel Garba jami’in ‘dan sanda ne wanda a watan gobe aka sa rai zai yi aure a Azare. Sai dai Allah (SWT) bai nufa zai auri masoyiyar ta sa ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon matasan da suka shiga hannu yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa ASP Abdulmuhyi Bagel Garba kani ne ga kwamishinar wuta, kimiyya da fasaha ta jihar Bauchi, Maryam Garba Bagel.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.