Masu yi da gaske: Bidiyon wani mutum yana yiwa matarsa kyautar jirgi ya jawo cece-kuce

Masu yi da gaske: Bidiyon wani mutum yana yiwa matarsa kyautar jirgi ya jawo cece-kuce

  • Masoya biyu ma'aurata, Masoud da Stephanie Shojaee, sun nunawa mutane cewa komai tsufan aure, kada soyayya ta gushe
  • A cikin wani faifan bidiyo da matar ta yada ta yanar gizo, mijin ya ba ta jirgin sama nata na kanta a matsayin kyautar farkon Kirsimeti
  • Wannan kyauta ya jawo cece-kuce a kafofin sada zumunta, inda mutane da yawa suka bayyana ra'ayoyinsu akai

Shahararrun ma'aurata a kafar Instagram, Masoud da Stephanie Shojaee, sun sa mutane magana yayin da matar ta yada wani gajeren bidiyonta da mijinta.

A cikin gajeren faifan bidiyon, an fito da matar ne daga cikin wata mota kirar Rolls Royce yayin da Masoud ya rufe idonta. A gabanta kuwa, ga wani jirgi mai zaman kansa.

Mutumin da ya yiwa matarsa kyautar jirgi
Masu yi da gaske: Bidiyon yana yiwa matarsa kyautar jirgi saboda wani dalili | Hoto: @stephshojaee
Asali: Instagram

Babbar kyauta ga matarsa!

Kara karanta wannan

Amaryata ta yi barazanar kashe uwar gidana da yayana, dan Allah a rabani da ita, Miji ya faɗawa kotu

Lokacin da aka bude idonta, sai matar ta rungume mijinta cikin murna da annashuwa. Ta rubuta cewa bayan shekaru 11, mijinta har yanzu ya san hanyar da zai ba ta mamaki da farin ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Stephanie ta bayyana cewa jirgin kyauta ce mai ban mamaki a gare ta. Ta kara da cewa ta so jan kafet da aka shimfida mata a bakin jirgin don karramawa.

Kalli bidiyon:

Yaya ba ki suma ba?

Mutane da dama da suka yi sharhi game da wannan kyauta sun yi mamakin yadda ta samu nutsuwa kuma ba ta suma ba da ganin irin wannan babban lamari.

Menene sana'ar wannan miji?

Duba ga bayanan mijin ya nuna cewa yana aikin sayar da gidaje ne kuma shine shugaban kamfanin SHOMA GROUP, kamfanin da aka kafa inji bayanansa na Instagram a shekarar 1988.

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: Gobara ta yi kaca-kaca da katafaren kamfani a jihar Kano

Lokacin da @instablog9ja ya sake yada bidiyon, 'yan Najeriya sun tofa Albarkacin bakinsu. Wasu dai sun ce mutumin ba wai kawai kai makura yayi a nuna soyayya ba, shi ne ma kololuwa a fannin.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin maganganun 'yan Najeriya kamar haka:

@vivian__chidimma ya ce:

"Omo ko wandi ban taba karba ba."

@pwesshydance ya ce:

"Mazan turawa suna da nuna kauna ba irin wadannan yaushe zaki zo ba."

@preccyclara ya ce:

"Kamar dai na raka wasu mata duniya ne. Na gode Allah da ya bani rayuwa."

@__ocube ya ce:

"Omo sun siya wa wannan baiwar Allah PJ amma bata yi tsalle ta yaga kayan jikinta ba, ka ga kenan talauci ne ke sa 'yan matan mu ke ihun saboda basu zoben nuna sha'awar aure."

Bayan auren mata biyu masu juna biyu, ango ya ji dadin zama dasu, ya ce dole ya yi kari

A wani labarin, wani wanda ya auri mata biyu a rana guda mai suna Prince Erere Nana ya shawarci maza da su auri mata fiye da daya, matakin da ya ce zai dakile magudi a gidan aure.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano zai angwance da galleliyar budurwa, tsohuwar zumansa nan kusa

Mutumin dan Najeriya daga kauyen Orhokpokpor da ke Delta ya jawo cece-kuce a intanet bayan sanar da gayyatar daurin aurensa inda ya bayyana cewa zai auri mata biyu masu juna biyu.

Da yake magana a wajen rufe bikin aurensa na gargajiya da matansa, Erere ya shaida wa BBC News Pidgin cewa shi ne mutumin da ya fi kowa farin ciki a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.