Masu gaskiya biyar da suka mayar da kudaden da suka tsinta ga masu shi a 2021
- Abu ne mai matukar wahala samun mutane masu gaskiya, waɗan da suke kwatanta adalci a harkokin su na yau da kullum
- A dai-dai lokacin da shekarar 2021 ke gab da ƙarewa, mun tattaro muku wasu mutum biyar masu gaskiya da suka mayar da kudaden da suka tsinta
- Halin gaskiya da rikon amana ya fi karfin mutum ya saka kudi ya siya, kuma kafin samun mai gaskiya sai an tona
A zamanin da muke ciki mutane kalilan ne zasu tsinci maƙudan kuɗaɗe da aka tura asusun bankin su bisa kuskure kuma su mayar wa mai shi.
Wannan shine halin gaskiya da tsoron Allah da waɗan nan mutum biyar ɗin suka yi a Najeriya cikin shekarar 2021.
Legit.ng Hausa ta tattaro muku waɗan nan yan Najeriya biyar da suka mayar da makudan kudi ga masu shi.
1. Julius Eze ya mayar da miliyan N2.5m da akai kuskuren tura wa asusun bankinsa
A ranar 11 ga watan Agusta, 2021 Julius Eze ya samu sakon shigowar makuɗan kudi asusun bankinsa har miliyan N2.5m ba zato ba tsammani.
Kamar yadda Legit.ng ta rahoto muku, kuɗaɗen sun shiga asusun wannan bawan Allah ne kashi-kashi, N500,000, N1,000,000 da kuma N1,000,000.
Kasancewar bai yi tsammanin kudi haka ba kuma ba su yi da wani zai tura masa ba, Julius ya shiga binciken neman asalin wanda ya yi kuskuren tura masa kudin.
Awanni kaɗan Julius ya yi nasarar gano mai kudin kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya mayar masa da kudinsa. Ya tura hoton tabbatarwa a shafinsa na sada zumunta.
2. Olasupo Abideen ya mayar da dala $2397 (N991,159.50) da aka yi kuskuren tura masa
Haka nan mun gano wani mutum mai gaskiya, Olasupo Abideen, wanda ya mayar da kimanin dala $2397 (N991,159.50) da kamfanin da yake aiki ya yi kuskuren antaya masa a asusun banki.
Bisa halin kirkin da ya nuna, an baiwa Abideen lambar yabo ta Gani Fawehinmi Integrity awards 2021. Shi ya bayyana a shafinsa na facebook:
"Na yi farin ciki da samun wannan lambar yabo da aka kirkira domin girmama jigo na ƙasa, marigayi Gani Fawehinmi."
"Kuma wannan wata dama ce gare ni na tuna wa yan uwana matasa, mu saka gaskiya, rikon amana a harkokin mu na yau da kullum."
3. Dalibin aji biyu a jami'a, Philip Okapor, ya mayar da jaka cike da makudan kudade
Philip Okapor, ya banbanta da sauran mutanen wannan zamanin, inda ya zaɓi neman mai jakar da ya tsinta a kan hanya.
Jakar da dalibin ya tsinta na ɗauke da kuɗaɗe, amma maimakon ya yi amfani da su, sai ya zaɓi mayar wa asalin mai shi.
A wani rubutun Facebook da aka yi domin farin cikin halin da ya nuna, makarantarsu, jami'ar Benin tace:
"Ku haɗu da Philips Okapor, dalibin aji biyu dake karatun Microbiology, wanda ya samu lambar yabo kan nuna hali abin koyi. Ya tsinci jakar aje kudi ta ɗan uwansa ɗalibi ɗauke da kudi."
4. Direban Keke Napep Mallam Tutu, ya mayar da N500k ga mai shi a Kano
Wani direban Keke Napep a jihar Kano, Mallam Tutu, ya nuna halin gaskiya abin misali, yayin da ya mayar da N500,000 ga fasinja, wanda ya mance da su a Keke Napep.
Mallam Tutu, ya yi abinda zai wahala abokan aikinsa na direbobin Napep su iya yi. Ya samu kyautar N500k saboda gaskiyarsa, kamar yadda Legit.ng ta rahoto.
5. Direba Emmanuel Eluu ya mayar da dala $40,000 (N16,442,000) ga fasinja
Binciken mu kan irin waɗan nan mutane ba zai kammalu ba har sai mun ambato Emmanuel Eluu, direbam bas mai gaskiya a jihar Legas.
Ya mayar da makudan kudi $40,000 (N16,442,000) da wani fasinja ya mance a motarsa. Kuma mai kudin wani sanannen ɗan Najeriya ne dake kan hanyar zuwa Patakwal.
Ba abune mai sauki ba kwatanta irin wannan hali na gaskiya, amma abu ne mai kyau dake haifar da ɗa mai ido.
Hali mai kyau dake tattare da ɗai-daikun mutane masu gaskiya, ya fi ƙarfin ka siya da kudin ka.
A wani labarin kuma Muhimman abubuwa 4 da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu
Jagoran yan bindiga, wanda ake ganin ya addabi jihar Zamfara da wasu yankuna, Bello Turji, ya nemi a zauna zaman sulhu.
A ciki wasikar da ya aike wa shugaba Buhari, gwamna Matawalle, da sarkin Shinkafi, Turji ya nemi a cika wasu sharuɗɗa 4.
Asali: Legit.ng