Albashi ba adadi: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da limamin Harami, Sheikh Sudais
Sheikh Abdurrahman As-Sudais shi ne shugaban limaman masallacin Harami da ke garin Makkah a kasar Saudiyya, shahararre ne wajen rera kira'ar Al-Qur'ani mai girma, wanda kadan ne daga cikin musulmai basu san muryarsa ba.
Kamar yadda duniya ke gani, limaman masallacin Harami a kasar Saudiyya na yin rayuwarsu ta jin dadi ta hanyar samun gata daga masarautar Saudiyya.
Kafar sadarwa ta Al-Haramain Sharifain takan nuna takaitattun bidiyo da kuma yada hotunan abubuwan da ke faruwa a masallatan Harami guda biyu, wanda anan ake yawan ganin malamai cikin sutura ta kawa da rayuwa mai kyau.
A cikin wannan rahoton, Legit.ng Hausa ta yi duba zuwa ga takaitaccen tarihin daya daga cikin manyan malamai kuma limami a Harami; Sheikh Abdulrahman As-Sudais
1. Asali da tushensa
Sheikh As-Sudais ya fito ne daga kabilar Anazzah daga cikin larabawan Saudiyya, ya kuma haddace Al-Qur'ani tun yana dan shekara 12 a duniya, ya girma a garin Riyadh ta kasar Saudiyya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Karatu
Ya yi karatu a makarantar firamare ta Al Muthana Bin Harith, sannan ya yi karatu a Cibiyar Kimiyya ta Riyadh wadda a cikinta ya kammala a 1979 da da sakamako mai kyau, inji Dubai International Qur'anic Award.
Ya samu digiri a fannin shari'a a jami'ar Riyadh a shekarar 1983, inda ya samu digirinsa na biyu a fannin ilimin addinin musulunci a Kwalejin Shari'a ta Imam Muhammad bin Saud a jami'ar Musulunci a 1987.
3. Aiki
Sheikh As-Sudais ya yi aiki a jami'ar Umm al-Qura a 1995, inda kuma anan ya samu digirin digirgir na Ph.D. a fannin Shari'ar Musulunci a lokacin da yake aiki a can a matsayin mataimakin farfesa bayan ya yi aiki a jami'ar Riyadh.
As-Sudais ya karbi aikin limanci a shekarar 1984, a lokacin yana da shekara 24 kacal, kuma ya gudanar da hudubarsa ta farko a Masallacin Harami da ke Makkah a watan Yulin 1984. Ya kasance tare da Sheikh Shuraim a wannan matsayi na tsawon shekaru.
Ya karbi lambobin yabo a bangarori daban daga kasashe daban-daban, irinsu Dubai saboda irin mutuncinsa a idon duniyar musulmi.
4. Kundin rayuwarsa
A rayuwarsa ya ziyarci kasashe da yawa a duniya, kamar Pakistan, Malaysia, Burtaniya da India; a kokarinsa na yada akidun muslunci da tarbiyyar muslunci.
An nada shi “Shugabancin Masallatan Harami guda biyu a matsayin minista” bisa umarnin masarautar Saudiyya a ranar 8 ga Mayu 2012, kamar yadda Al-Haramain ta ruwaito.
Shehin Malamin yana da mata daya. An ce matarsa 'yar dangi ne, sunanta Fatima Bint Ali As-Sudais. Yana da 'ya'ya; hudu maza, biyar mata.
5. Albashinsa
Wata kafar yanar gizo da ke tattaro bayanai kan rayuwa a kasar Saudiyya mai suna Life In Saudi Arabia ta bayyana irin kudaden da ake biyan shehin malamin tare da sauran limamai.
A cewar kafar, gwamnatin Saudiyya ta ce ba za ta biya limaman masallacin Haramin wani kudin albashi ba.
Inji masarautar Saudiyya, aikin da limaman masallatan Harami ke yi ba za a iya kwatanta shi da kudi ko dukiya ba, sai dai, Saudiyya na ba su holokon cekin banki ne domin su cika su ciri irin kudaden da suke so duk yawansu.
6. Yawan dukiyarsa, zunzurutun kudi da daraja a idon duniya
Duk da cewa ba a bayyanawa jama'a darajar duniyar Imam Abdulrahman Al-Sadais ba. Akwai kiyasi daban-daban game da dukiyarsa wanda mafi yawan abin da aka raja'a akai ya kai kusan dala miliyan 1.
Mutane da yawa na cewa haqiqanin darajar arzikin da Sheikh Imam Abdulrahman Al-Sadais ya mallaka ita ce girmamawar da yake samu daga kowa a duniya.
Takaitaccen tarihin Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar
A wani labarin kuwa, a Najeriya, kasa mai yawan musulmai kusan 50%, a rana mai kamar ta yau, 2 ga watan Nuwambar 2006 ta shaida samun sabon sarkin Musulmi a kan karagar shugabancin al'amuran musulman kasar.
Alhaji Muhammadu Sa'adu Abubakar III, shine sarkin Musulmi, wanda aka yi wa nadin rawani a ranar 2 ga watan Nuwamba a shekarar 2006, jim kadan bayan rasuwar marigayi sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Maccido.
Alhaji Muhammadu Sa'adu na daya daga cikin magadan karagar mujaddadi Shehu Usmanu Dan Fodiyo wanda ya yi jihadin yada addinin Islama a yankuna daban-daban na Najeriya.
Asali: Legit.ng