Hotunan tsohon mataimakin gwamna a Najeriya da ya koma noman doya shi da matarsa

Hotunan tsohon mataimakin gwamna a Najeriya da ya koma noman doya shi da matarsa

  • Wani tsohon mataimakin gwamna a jihar Anambra, Emeka Sibeudu, ya samu yabo a yanar gizo bayan da ya nuna babban rumbun da ya ke da shi na doya
  • Tsohon mataimakin gwamnan ya ce ya samu nasarar kammala aikin ne da taimakon da ya samu daga matarsa
  • ‘Yan Najeriya da dama da suka yi martani kan hotunansa sun ce hakan ya tunatar da su irin noman da iyayensu suka taba yi

Wani tsohon mataimakin gwamna a Najeriya, Emeka Sibeudu, ya kammala aikin noman doya a gonarsa. Sashen watsa labarai na Anambra ne ya yada hotunan aikin noman da ya kammala.

A cikin faifan bidiyo da aka yada, ana iya ganin tsohon mataimakin gwamnan jihar yana aiki yayin da yake kokarin jera sauwowin doyan da dama.

Kara karanta wannan

El-Rufai na shan caccaka bayan da aka gano ya saba umarnin Buhari, ya yi amfani da Twitter

Hotunan tsohon mataimakin gwamna a Najeriya da ya koma noman doya shi da matarsa
Tsohon mataimakin gwamna manomin doya | Hoto: Anambra Broadcasting Service
Asali: Facebook

Matata ce ta tallafeni a aikin gonata

A cewar kafar da ta yada hotunan, tsohon mataimakin gwamnan ya ce:

"Godiya ga ubangiji yau mun gama daure doya, da taimakon uwargida, girbi me kyau."

A lokacin rubuta wannan rahoto, rubutun ya tattara fiye da martani dari tare da dubban dagwale.

Kalli hotunan:

Martanin jama'a

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a:

Gimbiya Amaka ta ce.

“Ya tuna min da mahaifina da ya mutu, haka yake shirya doya a jikin rumbu...yayi kyau sosai...musamman idan na shiga ciki don in saci doya ba tare da sanin ya dawo daga shago ba yana jerawa..yakan yi tsawa ne kawai...?"

Johnpatrick Elodi ya ce:

"A zamanin da, dukiyar mutum takan ta'allaka ne da yawan doyarsa!"

Sunday E. Okoroafor ya ce:

Kara karanta wannan

Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa

"Gaskiya ya nuna cewa ya fito daga Umunze.... Al'ada ce kuma ya san yadda ake yi... Sannu da kokari yallabai."

Bidiyon yadda wani dan Najeriya ke noman doya a cikin buhunna ba a gona ba

A labar makamancin wannan, Legit.ng ta samo bidiyon wani dan Najeriya ya shiga harkar noma ta wata hanyar da ba a saba gani ba.

Mutumin da ba a bayyana ko wanene shi ba, a bidiyon da Ayo Ojeniyi ya yada a Facebook, ya nuna yadda ya shuka dashen doya 4000 a wani fili a jihar Anambra. Yana shuka amfanin gonarsa a cikin buhuhuwan siminti.

A cikin bidiyon, ya karfafawa mutane su gwada irin wannan tsarin nashi. Ya ci gaba da bayyana cewa mutum na iya shuka doya sau biyu a shekara da wannan dabarar noma kuma ba a bukatar babban fili.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.