Cika shekaru 15 kan mulki: Takaitaccen tarihin Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar
- A yau ne sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar ya cika shekaru 15 a karagar mulki
- An nada shi ne shekarun da suka gabata bayan rasuwar dan uwansa, Sarkin musulmi Muhammadu Maccido
- Mun tattaro muku tarihinsa, da kuma irin mukaman da ya rike yake kuma rike dasu a halin yanzu
A Najeriya, kasa mai yawan musulmai kusan 50%, a rana mai kamar ta yau, 2 ga watan Nuwambar 2006 ta shaida samun sabon sarkin Musulmi a kan karagar shugabancin al'amuran musulman kasar.
Alhaji Muhammadu Sa'adu Abubakar III, shine sarkin Musulmi, wanda aka yi wa nadin rawani a ranar 2 ga watan Nuwamba a shekarar 2006, jim kadan bayan rasuwar marigayi sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Maccido.
Alhaji Muhammadu Sa'adu na daya daga cikin magadan karagar mujaddadi Shehu Usmanu Dan Fodiyo wanda ya yi jihadin yada addinin Islama a yankuna daban-daban na Najeriya.
Haihuwarsa da tasowarsa
An haifi Sa'adu Abubakar a ranar 24 ga watan Agusta shekarar 1956, a garin Sokoto ta Arewacin Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ce shi da ne ga Sarkin Musulmi na 17, Alhaji Siddiq Abubakar III, wanda ya shafe sama da shekaru hamsin a matsayin Sarkin Musulmi a Najeriya, inji The Muslim 500.
Ya yi karatun sakandare a Kwalejin Barewa da ke Zariya, jihar Kaduna, kafin daga bisani ya tafi makarantar horar da sojoji ta NDA a shekarar 1975.
Aikinsa
Abubakar ya samu mukamin Laftanar na biyu a shekarar 1977 kuma ya yi aiki a manyan jami’an tsaro na Armored Corps.
Ya shugabanci sashin tsaron shugaban kasa na rundunar sojoji da ke gadin shugaban mulkin soja na wancan lokacin wato Janar Ibrahim Babangida a karshen shekarun 1980.
Yayi aiki a rundunonin soji daban-daban a cikin wa wajen Najeriya, inda ya yi ritaya a mukamin burgediya janar a shekarar 2006, Daily Trust ta ruwaito.
Zamansa sarkin Musulmi
A ranar 2 ga Nuwamba, 2006, Abubakar ya hau karagar mulki bayan rasuwar dan uwansa, Muhammadu Maccido, wanda ya rasu a jirgin ADC mai lamba 53.
Sauran mukamansa da nasarorinsa
A matsayinsa na Sarkin Musulmi, shi ne jagoran darikar Sufaye na Kadiriyya a Najeriya.
Shi ne kuma shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA).
A shekarar 2015, Muhammadu Sa'adu Abubakar III ya shiga cikin mutane 10 da suka samu nasarar shiga bugu na farko na Global Seal of Integrity (GSOI).
A ranar 22 ga Agusta 2019, an nada shi a matsayin mai gudanarwa na kungiyar Council of Religion for Peace (CRP), kamar yadda Wikipedia ta tattaro.
BBC ta ruwaito cewa, Sarkin musulmi tare da wasu manyan Najeriya sun fito a jerin mutane masu tasiri a cikin al'ummar musulmin duniya.
Lambobin girma
Mai alfarman ya samu lambar girma da digirin karrama wa daga jami’o’i kamar; Jami’ar Ahmadu Bello, UNIBEN, jami’ar Ibadan, jami’ar tarayya da ke garin Abuja.
Har ila yau jami’ar jihar Legas da ta jihar Anambra da jami’ar Usman Danfodio sun taba karrama shi.
Sarkin Musulmi ya bayyana 'yan Boko a matsayin matsalar Najeriya
Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana cewa ’yan boko da masu fada aji a kasar nan sune matsalar Najeriya.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya fadi hakan ne a yayin wani taron wanzar da zaman lafiya da gina kasa da Kwamitin Shirya Da’awah na Kasa ya shirya karo na uku a Jihar Gombe.
Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, a yayin taron ne kwamitin wanda ya hada mabiya addinin Kirista da Musulmi ya tattauna matsalolin da ke hana ruwa gudu wajen samun zaman lafiya a kasar nan.
Asali: Legit.ng